✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wata mata ta kamu da cutar Kurona a Legas

Mahukunta a jihar Legas sun tabbatar da samun wata mata ‘yar Najeriya  mai shekara 30 da ta kamu da cutar murar mashako ta kurona wato…

Mahukunta a jihar Legas sun tabbatar da samun wata mata ‘yar Najeriya  mai shekara 30 da ta kamu da cutar murar mashako ta kurona wato COVID-19 a ranar Talata.

Matar bata cikin wadanda suka yi alaka da dan kasar Italiyar da ya shigo da cutar a karon farko a Najeriya sai dai ta shigo kasar ne daga kasar Birtaniya a ranar 14 ga watan Maris 2020.

Zuwa yanzu dai ana kula da lafiyarta a babba asibitin Mainland a cikin garin Legas.

A ranar Litinin ne karamin Ministan Ma’aikatar Lafiya ta Najeriya Adeleke Mamora, ya shaida wa ‘yan jaridu cewa wani likita dan Najeriya mai suna Olumide Okunuga, da ke zaune a kasar Italiya ya rasu bayan ya kamu da cutar Kurona.

Ya ce, likitan ya samu cutar ne a lokacin da ya je bulaguro kasar Canada, dan haka kada ‘yan Nigeriya su rudu da masu cewa cuta bata kama bakaken fata ko kuma ‘yan Najeriya, inda ya yi kira da a ci gaba da daukar matakin kariya.