✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wata mata ta shiga hannu kan satar tumatir a kasuwa

Jami'an tsaro sun ce matar ta amsa laifinta.

An kama wata mata mai shekara 32 bisa zargin satar kwandon tumatir da tattasai a Jihar Kwara.

Lamarin ya faru ne a Kasuwar Kulende da ke Karamar Hukumar Ilorin ta Kudu a ranar Laraba, bayan rahoton da ’yan kasuwar suka kai ga jami’an hukumar tsaro ta sibil difens.

Tuni jami’an hukumar suka shiga tsakani don kwantar da tarzomar da ta tashi a kasuwar sakamakon kama matar.

Kakakin hukumar, Ayeni Olasunkanmi wadda ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce wadda ake zargin ta saci “kwandon tumatir da na tattasai ta amsa laifin ta kuma za a dauki matakin shari’a a kanta nan ba da jimawa ba.”

An ruwaito cewar matsalar sace-sace a kasuwar ta zama ruwan dare tsakanin ’yan kasuwar.