✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wata ta kashe mijinta da tabarya a Jigawa

Rigima ta kaure a tsakaninsu, inda ake zargin matar da kwadawa mijin tabarya.

Rundunar ’yan sanda a Jihar Jigawa, ta sanar da fara gudanar da bincike kan wata mata da ake zargi da kashe mijinta bayan da wata sa’insa ta shiga tsakaninsu.

Rundunar ta ce ta samu rahoton aukuwar lamarin yayin da wani mutumin kauyen Karaftayi da ke Karamar Hukumar Dambatta ya shigar mata da korafi.

Ta ce mutumin ya sanar da cewa ringima ta kaure a tsakanin mijin da matarsa, inda ake zargin matar da kwadawa mijin na ta tabarya.

Yayin zantarwarsa da sashen Hausa na BBC, Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar, ASP Shitu Lawal Adam ya ce jami’ansu sun garzaya gida inda suka tarar da mijin yashe a kasa.

ASP Shitu ya bayan sun garzaya da shi Asibiti har ya fara karbar magani sai kuma rai ya yi halinsa.

Sai dai ya ce har yanzu basu iya gano musabbabin faruwar lamarin ba a yayin da suke ci gaba da bincike.

Kazalika, ya ce za a gurfanar da matar a gaban Kuliya da zarar sun kammala bincike.