✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tankar dakon mai ta yi bindiga a Jos

Motar dakon man ta kama da wuta ne a nan take bayan ta fadi

Mutum daya ya rasu a sakamakon fashewar wata tankar mai a safiyar ranar Alhamis a garin Jos, Jihar Filato.

Fashewar tankar man ta kuma kona ababen hawa da gine-gine da wata makarantar koyon aikin likitan dabbobi a kusa da Shataletalen Polo da ke garin na Jos.

Ganau sun ce an tsinci gawar wani mutum a cikin lambatu, kuma ana kyautata zaton shi ne direban motar man da ta kama da wuta bayan tana makare da mai.

Aminiya ta gano cewa da misalin karfe biyar na Asubahin ranar Alhamis ne lamarin ya faru bayan motar ta kwace ta shiga wani gidan mai a kusa da makaratar koyan aikin likitan dabbobi.

Shaidun gani da ido sun ce motar ta kama da wuta ne a nan take bayan ta fadi, kuma jami’an hukumar kashe gobara sun kai dauki.

Kakakin ’yan sandan Jihar Filato, DSP Alfred Alabo, ya tabbatar da aukuwar iftila’in, sai dai ya ce ba shi da masaniyar yawan mutanen da abin ya ritsa da su.