✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wata zai yi rashin lafiya a Najeriya ranar Litinin — Masana

Masanin ya kuma ce za a sake samun rashin lafiyar a watan Nuwamba

Wani masanin ilimin taurari ya yi hasashen cewa Najeriya da wasu kasashen Afirka za su fuskanci kisfewar wata ranar Litinin, 16 ga watan Mayun 2022.

Farfesa Augustine Ubachukwu, wanda shi ne shugaban tawagar binciken Ilimin taurari na Jami’ar Najeriya da ke Nsuka (UNN) a Jihar Enugu ne ya bayyana hakan a hirarsa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN).

Masanin ya kuma ce hasashen na nuna kisfewa ta biyu za ta biyo baya a ranar biyu ga watan Nuwamban 2022.

Kazalika, ya ce kowanne wata, za a samu jinjirin wata da zai zagaye duniya ta tsakaninta da rana, daga nan kuma ya zagaye duniyar ta wani bangaren daban ya fito a cikakkensa.

Ya kuma ce idan aka samu abubuwa uku a sararin samaniya sun jeru da juna, ko shakka babu ko dai a samu kisfewar wata ko kuma ta rana.

Masana kimiyya dai sun cewa idan wata ya bi ta inuwar duniya shi ne ake samun kisfewarsa.