✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Watan Azumi: Za a rage farashin kayan abinci da kashi 75

Za a rage farashin nau’ika 30,000 na kayayyakin abinci da a watan Ramadan

’Yan kasuwa a Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) za su rage farashin kayayyakinsu daga kashi 25 zuwa 75 cikin dari a lokacin watan azumi na Ramalana.

Farashin da ’yan kasuwar za su rage zai shafi akalla nau’ika 30,000 na kayayyakin abinci da ake sayarwa a kasar.

Kamfanin Dillancin Labaran Kasar (WAM), ya ce kayayyakin sun hada da shinkafa, nama, sukari da sauran kayayyakin da aka fi amfani da su a lokacin azumi.

Kafar labarai ta Arab News ta ruwaito Ma’aikatar Tattalin Arzikin UAE na cewa za ta yi zagaye 420 na sa ido domin tabbatar da shaguna sun bi sabuwar dokar.

Darakta a Ma’aikatar, Marwan Al-Sboosi, ya ce sun gana da ’yan kasuwa tare da gargadin su kar su kara farashin kayan masarufi a lokacin azumin.

Al-Sboosi ya ce sun kuma gana da wakilan masu sayar da kayan itatuwa da na lambu na kasuwanni a babban birnin kasar domin tabbatar da wadatar hajarsu a lokacin watan mai tarin falala.

Alkalumma sun nuna cewa, a cikin watan azumi kadai, ana amfani da akalla tan 17,000 na kayan itatuwa da na lambu duk rana a Dubai, sai kuma tan 5,000 a Abu Dhabi, babban birnin kasar ta UAE.

A halin yanzu, ’yan kasuwa sun wadata kasar da tan dubu 130 na kayan itatuwa da na lambu yayin da ya rage sauran ’yan kwanaki kalilan a fara azumin watan Ramalana.