✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Watan gobe za a dawo haska shirin Labarina

An dakatar da shirin ne a zango na hudu tun bayan daina ganin Nafisat Abdullahi

A ranar daya ga watan Yuli mai kamawa ce ake sa ran za a ci gaba da haska fim din Labarina mai dogon zango.

Daraktan shirin, wanda kamfanin Saira Movies ke daukar nauyi, Malam Aminu Saira ne ya sanar da hakan.

A sanarwar da ya fitar, daraktan ya ce, “ASSALAMU ALAIKUM WA RAHMATULLAH. Muna sanar da ma’abota kallon wannan shiri na Labarina mai dogon zango cewa in sha Allah za mu cigaba da daukar zango na biyar da na shida. Muna kuma sa ran fara haska muku shi a wata mai kamawa (JULY 2022) in sha Allah. Muna ba ku hakurin akan dogon jira da kuka yi. Muna godiya ga kaunarku gare mu 🙏 Allah Ya bar zumunci.”

Idan ba manta ba, an dakatar da shirin ne a zango na hudu tun bayan daina ganin jaruma Nafisat Abdullahi, inda ta sanar da cewa ba za ta samu cigaba da fitowa a shirin ba, wanda wasu suke tunanin kamar matsala ce aka samu.

Sai dai yanzu shirin zai dawo, kuma ba tare da ita ba, wanda hakan ya sa masu kallo suke tsimayinsa domin ganin yadda za ta kaya.