✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Wawure N4.5bn: An sake gurfanar da daraktocin FIRS

Ana zargin manyan jami'an hukumar FIRS takwas da yin ruf da ciki kan kudaden.

Daraktocin Hukumar Tara Kudaden Shiga ta Kasa (FIRS) sun sake gurfana a gaban kotu kan handame Naira biliyan hudu da miliyan 500.

Hukumar Yaki da Ta’annati ga Tattalin Arziki (EFCC) ta gurfanar da daraktocin tare da wasu manyan manajojin FIRS ne bisa zagin aikata laifuka 42 na almundahana da karkatar da kudaden.

“Kun hada baki kun boye haramtattun kudaden da aka samu hanyar rashawa da zamba da kuma rufa da ciki, wadanda laifuka ne,” inji alkalin Babbar Kotun da ke zamanta a Abuja, Mai Shari’a Toyin Bolaji Adegoke.

Amma wadanda ake zargin sun musanta laifin da ake tuhumarsu da aikatawa.

A don haka Kotun ta ba da belinsu a kan Naira miliyan 100 kowanne mutun daya

Ta kuma shardanta wa kowannensu ya kawo mai tsaya masa, wanda shi kuma wajibi ne ya kasance dan Najeriya da ya mallaki gida a yankin da kotun ke da iko, sannan ya kawo shaidar biyan haraji.

Wajibi ne kuma su mika wa kotun takardun fasfo dinsu, sannan su nemi izinin kotu kafin su yi tafiya zuwa kasar waje.

Kakain EFCC, Wilson Uwujaren ya ce an sake gurfanar da mutanen ne bayan sauya wa alkalin da ta fara sauraron shari’ar, Mai Shari’a Ijeoma Ojukwu, wurin aiki.

Wadanda ake zargin su ne Petar Hena, tsohon Babban Daraktan FIRS; Daraktan Kudin Hukumar, Mohammed Bello Auta; Daraktar Kudi da Ajiya, Amina Sidi; Umar Aliyu Aduka, Mai Binciken Kudin cikin gida; Mbura Mustapha, Mataimakin Manaja; Obi Okeke Malachy, Sahen Ayyuka; Obaje Napoleon Adofu, Shugaban Kasafi; Udo-Inyang Effiong Alfred (Officer II) da kuma Benjamin Jiya, Mataimakin Darakta.