✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda WhatsApp, Instgram da Facebook suka shafe awa 6 ba sa aiki

Wannan shi ne karo na biyu da shafukan suka daina aiki a 2021.

Kafofin sada zumunta na WhatsApp, Instagram da Facebook sun shafe tsawon awa shida ba sa aiki, wanda hakan ya jefa mutanen da ke amfani da su cikin damuwa.

Shafuka da manhajojin WhatsApp, Instagram da Facebook wadanda dukkanninsu mallakin kamfanin Facebook ne, wanda kuma shi ke gudanar da su, sun daina aiki ne da misalin karfe 5:00 na yammacin ranar Litinin.

Shafin WhatsApp wanda ake amfani da shi ta intanet, shi ne na farko da ya daina aiki kafin daga bisani manhajar ta waya ya daina; sannan Facebook da Instagram suka bi sahu.

Lamarin ba iya Amurka, Birtaniya da nahiyar Turai kadai ya shafa ba, har sauran sassa na duniya.

Masu amfani da manhajoji ko shafukan WhatsApp, Instagram da Facebook, sun kasa turawa ko karbar sakonni ta nan, amma sauran kafafen sada zumunta irin su Twitter, TikTok, da Telegram suna aiki babu wata matsala.

Wannan shi ne karo na biyu da kafafen suka daina aiki a cikin kasa shekara guda, ko a ranar 19 ga watan Maris 2021, kafafon sun samu irin wannan matsala inda suka daina aiki har na tsawon sa’a biyu.