✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

WHO ta ba Bauchi tallafin rigakafin cutar Kwalara

An yi kira da a ba wa harkar tsaftar muhalli muhimmanci.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayar da tallafin rigakafin cutar kwalara guda miliyan 1.5 ga Jihar Bauchi.

Dokta Rilwanu Mohammed, Shugaban Hukumar Bunkasa Kiwon Lafiya a Matakin Farko (SPHCDA) na Jihar, ya bayyana hakan a wajen fara bayar da rigakafin ranar Asabar a Bauchi.

  1. Mutum 145 ne za su shirya auren Yusuf Buhari da ’yar Sarkin Bichi
  2. ’Yan bindiga sun sako daliban makarantar Bethel 28 a Kaduna

Mohammed ya ce WHO ta bada gudummawar rigakafin ne don tallafa wa jihar wajen magance cutar kwalara.

“Bauchi na daga cikin jihohi 18 da ke da fuskantar barazanar barkewar cutar kwalara, saboda haka za a yi amfani da wannan gudummawar a yankunan da ke fama da cutar,” in ji shi.

Kazalika, ya ce wasu unguwanni a Kananan Hukumomin Dass da Toro wadanda cutar ba ta yi kamari ba, suma za su karbi kason na rigakafin.

Ya kuma gode wa WHO kan yadda ta ke ci gaba da tallafa wa Hukumar ta hannun gwamnati wajen magance matsalolin kiwon lafiya makamanciyar cutar kwalara.

Wakilin WHO, Alhaji Goni Ngala, ya ce barkewar cutar na shafar rukunin mutane daban-daban ciki har da yara ‘yan kasa da shekaru biyar.

“A ci gaba da kokarin da take yi na bayar da tallafin maganin kwalara, ofishin Hukumar Lafiya ta Duniya ya ba da gudummawar rigakafin don tallafawa wadanda abun ya shafa,” in ji shi.

A nasa jawabin, Hakimin Bauchi, Alhaji Nura Jumba, ya jaddada muhimmancin aiwatar da matakan tabbtara da tsaftar ruwan sha da kuma muhalli musamman a yankunan da abin ya shafa.

Jumba ya bukaci gwamnati ta jajirce wajen inganta aikin kwashe shara da kuma watsi da wuraren bahaya.

“Samar da tsaftataccen ruwa sha kyauta ga al’ummomin da abin ya shafa ciki har da wayar da kan al’umma game da tsaftace muhallansu zai taimaka,” in ji shi.