✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

WHO ta fara tattaunawa da Birtaniya kan sabon nau’in COVID-19

“WHO ta fara tattaunawa da Burtaniya tun 14 ga watan Disamba kan sabuwar cutar".

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta fara tattaunawa da gwamnatin Burtaniya bisa bullar wata sabuwar nau’in cutar COVID-19 mai matukar hatsari.

Wakilin WHO a Rasha, Melita Vujnovic shi ne ya bayar da tabbatar da hakan a ranar Litinin, bayan a makon jiya Burtaniya ta sanar da bullar nau’in COVID-19 da ke iya yaduwa da sama da kaso 70 cikin dari a brinin London da kewaye.

A makon jiya ne Burtaniya ta sanar da bullar nau’in COVID-19 da ke iya yaduwa da sama da kaso 70 cikin dari a brinin London da kewaye.

Melita ya ce, “WHO ta fara tattaunawa da Burtaniya tun 14 ga watan Disamba tare da masana kimiyyar da suka gano sabuwar cutar.

“An bayar da shawarar cewa dukkan kasashe su yi gwajin kwayoyin halittarsu domin gano daga inda kwayar cutar ta samo asali da kuma yadda take yaduwa cikin gaggawa,” inji Melita, a tattaunawarsa kafar yada labarai ta Rossiya 24.

Gwamnatin Burtaniya dai ta dauki matakin hana yaduwar cutar ta hanyar wayar da kan jama’a yadda ya kamata, yayin da kasashe da dama suka hana jirage daga kasar sauka a cikinsu.

Kazalika, an samu rahoton bullar makamanciyar wannan nau’in cutar a wasu kasashen Turai, Australia da dama da ma Afirka ta Kudu.