✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wike ya hana ‘yan sanda kama shugabar NDDC

Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike ya hana ‘yan sanda kama tsohuwar shugabar Hukumar Habbaka yankin Neja Delta (NNDC) Joi Nunieh bayan sun yi wa gidanta.…

Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike ya hana ‘yan sanda kama tsohuwar shugabar Hukumar Habbaka yankin Neja Delta (NNDC) Joi Nunieh bayan sun yi wa gidanta.

Majiyarmu ta ce bayan ‘yan sanda sun yi wa gidan Joi Nunieh da ke garin Fatakwal kawanya domin tafiya da ita ne Wike ya kutsa cikin gidan ya dauke ta ya tafi da ita ya kuma umarci ‘yan sandan da su watse.

Hakan ya faru ne a ranar Alhamis din da ake jiran Nunieh ta bayyana a gaban kwamitin binciken zargin badakala a NDDC mai aikin habbaka yankin na Neja Delta.

A kwanakin baya, Nunieh ta zargi Ministan Neja Delta Godswill Akpabio da yunkurin cin zarafinta da kuma rashawa da saura abubuwa na saba doka.

Sai dai kuma mai magana da yawun Ministan, Aniete Ekong ya ce zargin kazafi ne da cin mutunci da neman zubar wa ministan kima.

Tuni gwamnatin Ribas ta yi alkawarin kariya ga Nunieh wadda ‘yar asalin jihar ce, a cewar wata majiya.

Kwamishinan watsa labarai na Jihar Ribas, Paulinus Nsirim ya ce “Ba za mu shiga rikicin hukumar ba amma kuma ba za mu bari a ci mutunci ‘yarmu ba. Hakkinmu ne mu kare mutuncin kowane dan Jihar Ribas ko da muna da bambancin jam’iyya”, inji Nsirim.