✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wike ya sasanta da Atiku —Ortom

Gwamnan ya ce dukkan matsalolin su na cikin gida ne, kuma za su warware su.

Gwamna Samuel Ortom na Jihar Binuwai, ya ce dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, sun sasanta ta Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike bayan sabanin da suka samu kan zabo abokin takarar Atiku.

A wata hira da ya yi da gidan talabijin na Arise, Ortom wanda na hannun Wike ne, ya ce tuni dan takarar shugaban kasar na PDP ya sasanta da Wike kan sabanin da ke kokarin aukuwa a tsakaninsu.

“Duk abin da nake so a kan (Wike), shi (Atiku) ya amince kuma suna magana da juna,” in ji Ortom.

Ya yi wannan batu ne a lokacin da yake bayyana dalilin da ya sa ba zai je bijire wa Atiku kan zabar Ifeanyi Okowa, a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa a zaben 2023 mai zuwa.

Ortom ya zargi Atiku da kin amince wa da shawarar da Wike ya bayar kan takwaransa na Jihar Delta a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar.

Sai dai Atiku ya yi martani ga Ortom da cewa ya ki amincewa da shawarar kwamitin PDP kan zaben dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar.

Da yake amsa tambayoyin ’yan jarida a Makurdi a ranar Litinin, dangane da martanin da Atiku ya yi na cewa, “Ba a yi zabe ba, zan iya ba ku kwafin rahoton kwamitin, kwamitin da ya gabatar da mutum ukun da aka zaba, gwamnan Jihar Binuwai ne ya jagoranta, Samuel Ortom.

“Sun ba da shawarar zabar mutum uku, don haka na zabo daya.

“Duk da haka gwamnan ya ce an riga an magance lamarin a cikin gida.”

Ortom ya ce, “Ba zan so in saba wa dan takararar na shugaban kasa ba, duk abin da ya faru daidai ko kuskure, na yarda da shi.

“Mu dangi daya ne, za mu nemo hanyar warware matsalarmu”