✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wike ya yi barazanar hana Atiku wajen taro a Ribas

Gwamnan ya ce muddin aka fusata shi, zai soke izinin

Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, ya yi barazanar soke izinin yin amfani filin wasa na Adokiye Amiesimaka da ke Fatakwal, babban birnin jihar, wanda ya ba dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar domin gangamin kamfen.

Gwamnan ya ce sama da wata daya ke nan Darakta-Janar din yakin neman zaben Atiku a jihar, Dokta Abiye Sekibo, na sintiri a filin gabanin taron da za su gudanar ranar 11 ga watan Fabrairu mai zuwa.

Wike ya ce sun ba da filin domin gudanar da taron ba tare da an biya su ko sisi ba, inda ya ce za a damka musu shi ana saura kwana biyu kafin ranar taron.

Sai dai yayin gangamin yakin neman zaben PDP a Karamar Hukumar Oyigbo da ke Jihar ranar Juma’a, Gwamnan ya ce Abiye ba shi da hurumin da zai karbe wajen tun ana saura wata daya kafin ranar taron nasu.

Ya ja kunnen dan siyasar da kada ya fusata su ta hanyar yunkurin karbe filin, wanda mallakin Gwamnatin Jihar ne tun ana makonni kafin ranar, in ba haka ba kuma su soke izinin.

“Babu wanda ya baka [Dokta Sekibo] damar amfani da wajen na tsawon wata daya. Saboda haka, duk ranar da ka kara zuwa kana kokarin cusa kanka a cikin filin, zan soke izinin ba tare da wani bata lokaci ba, kuma babu abin da zai faru. Idan ma wani abin ya faru, za mu yi murna mu ce a lokacinmu ne.

“Na san ba ku shirya yin wannan gangamin ba, kawai kuna neman uzuri ne, amma dole sai kun yi. Na san za ku debo hayar mutane, amma babu matsala, ku je ku kwaso su, mun ba ku wajen,” in ji Gwamna Wike.