✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wilberforce Juta: Jihar Adamawa na zaman makoki

Jihar Adamawa ta fara zaman makoki na kwana uku bayan rasuwar tsohon Gwamnan Tsohuwar Jihar Gongola, Ambasada Wilberforce Bafte Juta. Gwamna Umaru Fintiri yayin juyayin rasuwar…

Jihar Adamawa ta fara zaman makoki na kwana uku bayan rasuwar tsohon Gwamnan Tsohuwar Jihar Gongola, Ambasada Wilberforce Bafte Juta.

Gwamna Umaru Fintiri yayin juyayin rasuwar jigon a jam’iyyar PDP, ya yaba da kyawawan ayyukan mamacin wajen bunkasa rayuwa da ci gaban siyasa, wanda ya ce za a dade ana yabawa.

“Domin girmama dattijon, Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya ayyana zaman makoki na kwana uku daga Asabar 15 ga Agusta, 2020”, inji sanarwar da kakakin gwamnan, Humwashi Wonosikou ya fitar.

Marigayi Juta wanda shi ne gwamnan tsohuwar Jibar Gongola a 1983, ya kuma yi Jakadan Najeriya a Zimbabwe daga shekarar 2000 zuwa 2004.