✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wuraren da za a iya samun turnuku a zaben 2023

Aminiya ta yi nazari kan wuraren da ake fargabar samun tashin hankali

Adaidai lokacin da ya rage kwana 64 zaben Shugaban Kasa da na Majalisun Tarayya, akwai wasu wurare da ake ganin mai yiwuwa a fuskanci turnuku da tashe-tashen hankali masu nasaba da zaben, lamarin da ya jefa fargaba ga hukumomin tsaro da masu ruwa-da tsaki a harkar zabe.

Hukumar INEC ta sanya ranar Asabar 25 ga Fabrairun 2023, domin gudanar da zabubbukan Shugaban kasa da na Majalisun Tarayya.

Za a yi zabubbukan ne a tashoshin zabe 176,846 da ke a fadin kasar nan inda ake sa-ran masu rajistar zabe fiye da miliyan 84 za su kada kuri’a.

Yayin da zabubbukan ke karatowa, ana ci gaba da haduwa da tashe-tashen hankali masu nasaba da zabe.

Wata kididdigar jaridar Aminiya ta nuna mutum 24 aka kashe a bana, aka jikkata da dama.

Masharhanta sun bayyana abubuwan da suke ganin su ne kanwa-uwar-gami wajen rura wutar rikicen-rikicen, kamar: kalaman tunzura jama’a da furta kalaman kyama da yada labaran karya (musamman a kafofin soshiyal midiya) da batun ce-ce-ku-ce kan tikitin Musulmi da Musulmi a Jam’iyyar APC da batun malaman addinai marasa hakuri wajen sabani kuma suke farraka mabiya da batun shafa kashin kaji ga kabila ko addini da fadan cikin gida a jam’iyyu da ma rigingimun shari’a a wasu jihohin.

Jaridar Aminiya ta gano cewa daga ranar 3 ga Fabrairun 2019, hukumar zabe ta fuskanci harehare 53 da aka kai wa ofisoshinta inda yankin Kudu maso Gabas ke kan gaba a jadawalin.

A lokacin da yake magana kan lamarin, Shugaban Hukumar INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu, ya ce Jihar Imo ce kan gaba inda aka kai hare-hare 11 sai jihohin Osun da Enugu da Akwa Ibom da hare-hare bakwai kowacensu yayin da jihohin Abiya da Kuros Ribas kowacensu aka kai hare-haren hudu.

Sannan an samu wadannan hare-haren sau biyu a jihohin Anambra da Taraba sai kuma sau daya a jihohin Bayelsa da Ondo da Legas da Borno da Kaduna da kuma Ogun.

Bayan komawa mulkin farar hula a 1999, an gudanar da manyan zabubbuka shida. Rahotannin sun ce a 1999, mutum 80 aka kashe, inda a 2003, aka kashe mutum 100; yayin da a 2007, mutum 300 suka salwanta.

A 2011 ne kasar ta hadu da asarar rayuka mafi muni inda mutum 800 suka rasa rayukansu.

A zabubbukan 2015 an kashe mutum 100 yayin da a 2019, aka hallaka mutum 145.

A cikin rahotonta na baya-bayan nan, Cibiyar Tony Blair, ta nuna damuwar cewa zabubbukan 2023 na fuskantar barazanar tashetashen hankali daga rikicin Boko Haram da ’yan IPOB da ’yan bindiga.

Kudu maso Gabas

Na farko a jerin yankunan da za a iya samun rikici shi ne jihohi biyar na Kudu maso Gabas, sakamakon ayyukan masu fafitukar kafa kasar Biyafra (IPOB).

Kungiyar IPOB mai rajin ballewa daga Najeriya, ta yi ikirarin cewa babban burinta shi ne wanzar da kasar Biyafara mai cin gashin kanta, inda ta addabi jihohi biyar da ke shiyyar – Ebonyi da Enugu da Abiya da Anambra da Imo.

Ana zargin kungiyar da kashe jami’an tsaro da ’yan siyasa da sarakunan gargajiya da ma talakawa. Ana kuma dora alhakin lalata cibiyoyin gwamnati kamar ofisoshin ’yan sanda da na INEC da sauransu a kan mambobinta.

A ranar Larabar makon jiya wani mai suna Simon Ekpa, wanda ya yi ikirarin cewa dan koren jagoran kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu ne, ya ce zaben 2023 ba zai gudana a Kudu maso Gabas ba.

Aminiya ta gano yankin Kudu maso Gabas na da akalla mutum miliyan 11.49 da suka yi rajistar zabe.

Legas

Legas, za a iya fuskantar tankiya lura da yadda magoya bayan Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na APC da na takwaransa na LP, Peter Obi suke gwada kwanji da juna.

Har ila yau, taken nan na, “Mu kwace Legas daga hannun Yarbawa” da wadansu ’yan kabilar Ibo suke yi, wadanda suke ganin suna da yawa da karfin da za su juya alkibla a Legas, na kara tayar da kura a jihar.

A daya bangaren kuma, akwai wadansu Yarbawa, wadanda ke ganin lokaci ya yi da za a rage tasirin ’yan kabilar Ibo daga siyasar jiharsu ta asali.

Aminiya ta gano akwai sama da kuri’a miliyan bakwai a Jihar Legas.

Kaduna da Katsina da Sakkwato da Zamfara

Kamar shiyyar Kudu maso Gabas, yankin Arewa maso Yamma ma akwai kura lura da aika-aikar ’yan fashin daji. Lamarin ya fi muni a hudu daga cikin jihohi bakwai da ke shiyyar wato Kaduna da Katsina da Sakkwato da Zamfara.

Shiyyar ta kasance mafi yawan masu rajistar zabe a kasar nan inda take da kuri’a miliyan 22.67.

A Jihar Kaduna, ’yan siyasa da mazauna kananan hukumomin Birnin Gwari da Giwa, wadanda su ne kananan hukumomin jihar da lamarin ya fi muni, sun ce da wuya a gudanar da zabubbukan a galibin sassan kananan hukumomin biyu saboda aika-aikar ’yan fashin daji.

Baya ga batun ’yan fashin, Jihar Kaduna ta kasance jihar da ake samun rikicin zabe da na kabilanci.

A watan jiya an yi artabu a wajen gangamin yakin neman zaben dan takarar Shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar.

A shekarar 2011 a rikicin da ya biyo bayan zaben Shugaban kasa, inda jihohi 12 suka fada cikin rikicin, daruruwan rayuka sun salwanta, inda aka fi kashe mutane a jihar ta Kaduna. Aminiya ta gano cewa baya ga kalubalen ’yan fashin daji da ya samu gindin zama a Jihar Zamfara, jihar na fama da barazanar ’yan bangar siyasa.

A watan Oktoba, rikici ya barke tsakanin magoya bayan Jam’iyyar PDP da APC, inda ya yi sanadiyar mutuwar mutum daya yayin da wadansu 18 suka jikkata.

A Jihar Katsina, Aminiya ta gano cewa kananan hukumomin batsari da Jibiya da Faskari da Safana da kankara da danmusa da Sabuwa da Funtuwa da kuma dandume na fuskantar kalubalen ’yan fashin daji.

Kano

Ana zaman dar-dar a Jihar Kano a tsakanin magoya bayan Jam’iyyar APC mai mulki da na NNPP.

Shugabannin Jam’iyyar NNPP sun yi barazanar cewa ba za su rattaba hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiya ba saboda kalaman tunzurawa na Shugaban Jam’iyyar APC, Abdullahi Abbas.

Idan za a iya tunawa, a shekarar 2019, jihar ta fuskanci tashe-tashen hankalin zabe da ya kai ga salwantar rayukan jama’a.

Benuwai da Filato da Taraba

Rikice-rikice kabilanci da na manoma da makiyaya da suke faruwa sun sanya jihohin Benuwai da Filato da kuma Taraba a matsayin yankunan da za a iya samun turnuku a zaben 2023.

A Jihar Benuwai wuraren da ake fargabar samun matsalar tsaro su ne Katsina-Ala da Ukum da Guma da Ado da Logo da wasu sassan karamar Hukumar Makurdi.

Sauran kananan hukumomin jihar mai taken ‘Akushin Najeriya,’ sun hada da Gwer ta Yamma da Gboko da Gwer ta Gabas da bandekiya da kuma Okokwu.

Akwai bayanan da ke cewa, a Jihar Taraba, mayakan Boko Haram da dama da suka kaura daga Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma, sun tare a can.

Ita ma Jihar Filato, ba a bar ta a baya ba wajen fama da rikicin kabilanci. kananan hukumomin Jos ta Arewa da Jos ta Kudu da kuma Bassa ne wuraren da ake fama da tashe-tashen hankali a jihar.

Borno

Koda yake ana ganin an rage kaifin Boko Haram sosai, amma harin da aka kai wa ayarin yakin neman zaben dan takarar Shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya sanya jihar ta kasance cikin jerin yankunan da ake tsoron aukuwar rikici a cikinsu lokacin zaben.

Magoya bayan Jam’iyyar PDP da APC na iya yin fito-na-fito a lokacin zaben.

Masani da AIG mai ritaya sun zayyana jihohi 15 da za a sanya ido kansu

Da yake sharhi a kan lamarin, wani babban malami a fannin Ilimin Zamantakewar Al’umma a Jami’ar Abuja, Dokta Abubakar Umar Kari, ya bayyana jihohi 15 a matsayin inda za a iya fuskantar ta da-zaune-tsaye.

Ya bayyana jihohin da suka hada da: Zamfara da Sakkwato da Katsina da Kaduna da Neja da Kano da Bauchi da Ribas da Delta da dukkan jihohi biyar da ke Kudu maso Gabas.

Ya ce, “Wuraren da ka iya fuskantar turnukun su ne: Rukunin (a): Jihohin da ’yan bindiga suke aika-aika kamar Zamfara da Sakkwato da Katsina da Kaduna da Neja. Sai Rukunin (b) na ’yan Boko Haram: Borno da Yobe.

Da Rukunin (c) masu fama da rikicin ’yan IPOB: Jihohin Abiya da Anambra da Enugu da Imo da Ebonyi. Da kuma Rukunin (d) wato jihohin da za a fi fafatawa wato Kano da Ribas da Bauchi da Delta sai kuma Rukunin (e) da suka hada da Legas (saboda yawan ’yan kabilar Ibo).

A nasa bangaren, Mataimakin Sufeto Janar na ’Yan sanda (mai ritaya), Ambrose Aisabor, ya sanya jihohin Legas da Osun da Ogun da Oyo da Ebonyi da Imo da Ribas da Delta da Borno da Benuwai da Kano da Zamfara da kuma Kaduna a matsayin jihohin da za a sanya wa ido.

’Yan awaren IPOB da na Yarbawa suna makarkashiyar hana zaben – Sufeto Janar

Da yake mayar da martani game da hareharen da aka kai a karshen makon jiya a yayin zaman bincike a zauren Majalisar Wakilai, Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya, Alhaji Usman Baba, ya ce kungiyoyin ’yan aware a kasar nan na kokarin kawo cikas a zaben 2023.

Dandaura Mustapha, Mataimakin Sufeto Janar, Mai Kula da Ayyuka, wanda ya wakilci Sufeto Janar din, ya ce yayin da kungiyar IPOB ke shirin kada a gudanar da zaben a Kudu maso Gabas, masu rajin ballewa daga kabilar Yarbawa su ma sun dukufa wajen ganin ba a a gudanar zabubbukan a yankin Kudu maso Yamma ba.

“Akwai kuma wadansu da ’yan siyasa da sauran masu ruwa-da-tsaki da ke daukar nauyinsu.

Haka kuma akwai batun ’yan siyasa da suka gaza kuma masu ganin ko ana-hamaza-ha-mata sai sun koma kan mukamansu da suka dukufa wajen hana INEC shirya wannan zabe,” in ji shi.

Batutuwa 10 da suke rura wutar rikicerikice

A yayin da gwamnati ke magance matsalar ’yan fashin daji da Boko Haram da IPOB, yawan kalaman nuna kyama da yada labaran karya a Intanet da takura wa ’yan hamayya da jam’iyyun da ke mulki suke yi a wasu jihohin da masu bangar siyasa da cin zarafin mata – su ke rura wutar rikici.

A tsokacinsa, Dokta Kari ya lissafa abubuwa takwas a matsayin abubuwan da suke haifar da matsala gabani da lokaci da kuma bayan zaben.

Ya ce, sun hada da: kalaman takala da na nuna kyama da labaran karya (musamman a kafafen sada zumunta) da rikicin tikitin Musulmi da Musulmi da ayyukan malamai marasa hakuri kuma masu farraka mabiya da kabilanci da addini da rigingimun cikin jam’iyya da kuma kararraki ko shari’o’in da ba sa karewa a wasu jihohin.

Sauran su ne hare-haren ta’addanci da ake kai wa mutane da kadarorinsu da kuma nuna kyama daga kungiyoyin ’yan ta’adda musamman irin su IPOB da ESN da wuce gona-da-iri da wasu lokuta tsammanin magoya baya fiye da kima da na dangi na wadansu ’yan takara da yakini ko akasin hakan na INEC za ta shirya zabubbukan cikin gaskiya da adalci da za su samu karbuwa daga jama’a.

Da yake magana kan al’amuran da suke haifar da rikici, Shugaban ’Yan sandan mai ritaya ya ce rashin kamanta gaskiya da daidaito a tsakanin jama’a ne kanwa uwar-gami wajen haifar da rikici.

Matakan da lallai ya kamata gwamnati ta dauka kafin zaben

Domin gudanar da zabubbukan ba tare da wata tangarda ba, malamin jami’ar da Mataimakin Sufeto Janar mai ritayar, sun amince cewa dole ne gwamnati ta nuna karfin ikonta, ta kuma kwato wasu yankuna da dama da ba sa hannunta, inda ’yan fashin daji da Boko Haram da ’yan IPOB ke iko da su.

Dokta Kari, ya ce a bai wa Hukumar INEC wuka da nama domin gudanar da zaben. A nasa bangaren, AIG mai ritayar, ya ce Gwamnatin Tarayya na da alhakin tabbatar da zabe mai cike da inganci.

An wallafa wannan labari ne a matsayin wani bangare na Rahotanni kan Rikice-Rikice da Zabubbuka tare da hadin gwiwa da Cibiyar Bunkasa Dimokoradiyya (CDD)