✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wutar lantarki ta babbake barawon wayar transfoma

Wutar ta babbake mutumin ne bayan da ya gama kwancewa wayoyin har ya ajiye su a kusa da tranfomar.

Wutar lantarki ta babbake wani mutum har lahira a lokacin da yake kokarin sace wayar wutar transfoma a kauyen Lambu da ke Karamar Hukumar Tofa ta Jihar Kano.
Wani mazaunin garin mai suna Naziru Lambu ya ce abin ya faru ne da misalin karfe 1 na dare kafin wayewar garin Laraba.

Ya bayyana cewa wutar ta babbake mutumin ne bayan da ya gama kwance wayoyin har ya ajiye su a kusa da tranfomar.

Ya ce wasun ’yan garin sun ce sun ji karar tartsatsin wutar lantarki a cikin dare da kuma ihun mutumin da ake kyautata zaton barawo ne kafin ya mutu.

Ya ce an tsinci gawar mutumin tana lilo, shi kuma ya rike waya a hannunsa.

Tuni dai jami’an tsaro da na kamfanin wutar lantarki ta KEDCO suka isa kauyen Lambu domin gudanar da bincike a kan abin da ya faru.