✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wutar Lantarki: ’Yan Boko Haram sun sake jefa Maiduguri a duhu

A baya ma dai birnin dai ya shafe kusan watanni biyu babu wutar tun bayan wani harin ’yan Boko Haram

Kasa da sa’o’i 48 bayan Hukumar Samar da Wutar Lantarki ta Kasa (TCN) ta dawo da hasken wutar lantarki a birnin Miaduguri na jihar Borno, ’yan ta’addan Boko Haram sun sake datse wani sashe na hanyar wutar.

Wani babban jami’in hukumar ne ya tabbatar da hakan ga Aminiya a wani rubutaccen sako da yammacin Asabar.

A cikin sakon dai jami’in ya ce, “Bayan dukkan kokarin da muka yi na dawo da wutar lantarki ga Maiduguri, ’yan ta’addan sun sake tayar da bam a jikin wata na’urar wutar lantarkin dake kan hanyar Damaturu zuwa Maiduguri mai karfin KVA 330 da misalin karfe 5:56 na safiyar ranar Asabar, 27 ga watan Maris 2021.”

A ranar Larabar da ta gabata dai an yi ta murna a Maiduguri bayan Kamfanin Rarraba Hasken Wutar Lantarki na Shiyyar Yola (YEDC) ya dawo da wutar bayan kokarin hukumar ta TCN.

Birnin dai ya shafe kusan watanni biyu a cikin duhu tun bayan da ’yan Boko Haram din suka kai hari a kan wata na’urar rarraba wutar dake garin Jakana a ranar 26 ga watan Janairun 2021.

Ko a lokacin da injiniyoyin TCN ke aikin dawo da wutar a kwanakin baya dai sai da motarsu ta taka wata nakiya da ’yan Boko Haram din suka binne da nufin hana su gyaran.