✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Xavi ya zama kocin Barcelona

An kai wannan matakin ne bayan cimma yarjejeniya tsakanin Barcelona da Al Sadd.

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta dauki tsohon wasanta Xavi Hernandez a matsayin sabon kocinta da zai ja ragamar horas da ’yan wasa.

Wannan na zuwa ne bayan kungiyar ta raba gari da Ronald Koeman wanda ta sallama a watan jiya saboda rashin katabus da ya yi.

Koeman wanda ya shafe watanni 14 kacal yana jagorantar horas da ’yan wasan, zamansa ya zo karshen ne a ranar 27 ga watan Oktoba bayan wasan da kungiyar ta La Liga ta sha kashi hannun Rayo Vallecano.

Wata sanarwa da Barcelon ta fitar na cewa a yanzu ta cimma yarjejeniya da Xavi na zama kocin kungiyar har zuwa karshen wannan kaka ta bana da kuma kaka biyu masu zuwa.

Tun a Yammacin Juma’a bayanai suka bulla cewa Barcelona na shirin sanar da sake kulla yarjejeniya da tsohon dan wasanta Xavi Hernandez, wanda a wannan karon zai koma gareta a matsayin mai horas da ’yan wasanta.

An kai wannan matakin ne bayan da aka cimma yarjejeniya tsakanin Barcelona da Al Sadd, kungiyar da Xavin ke horaswa a kasar Qatar.

Cikin sanarwar da ta fitar kungiyar ta Qatar ta ce Barcelona ta biya kudin sayen yarjejeniyar da ta rage tsakaninta Xavi, wanda ke horar da ’yan wasanta a Qatar tun shekarar 2019.

Yanzu haka dai ma’abota duniyar wasanni na dakon ganin yadda Xavi zai maido da karsashin tsohuwar kungiyarsa, zuwa makamancin lokacin da suke a matsayin ’yan wasa.

A lokacin da yake taka leda dai ana yi wa Xavi lakabi da ‘Maquina’, abinda ke nufi Inji da turancin Spain, dalilin kasancewarsa dan wasan tsakiya wanda ya yi fiye da fice wajen sarrafa kwallon kafa har tsawon shekaru goma.

Lokacin da Spain ta lashe gasar cin kofin duniya a shekara ta 2010, Xavi ya kafa tarihin baiwa abokan wasansa kwallon yayin da ake cikin wasa sau sama da 100 fiye da kowane dan wasa.

Yayin da kuma a gasar La Liga Lionel Messi ne kawai ya fi Xavi taimakawa wajen jefa kwallaye 117 a raga cikin wasanni 505 da suka buga.