✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Xi Jinping zai gana ido da ido da Biden a Indonesiya

Za su yi ganawa ta farko ta ido da ido tun bayan zaben Joe Biden.

Shugaban kasar Amurka Joe Biden zai gana da takwaransa na china Xi Jinping a birnin Bali na kasar Indonesiya yayin taron Kungiyar Kasashe Masu Karfin Tattalin Arziki na G20.

Wannan ganawa na zuwa ne a daidai lokacin da ake yin takun saka tsakanin manyan kasashen duniyar guda biyu.

Shugabannin biyu, wadanda za su yi ganawa ta farko ta ido da ido tun bayan zaben Joe Biden, za su tattauna kan yadda za a kawar da goggayar da ke a tsakanin kasahen biyu domin yin aiki tare.

Biden da Xi Jinping, wadanda suka riga suka yi magana sau da yawa ta wayar tarho tare da yin taron bidiyo.

Za su kuma tattauna jerin batutuwan kasa da kasa a ciki har a na Taiwan wanda shi ne tushen rikici tsakanin China da Amurka bayan ziyarar da kakakin majalisar dokokin Amurkan ta kai a Taiwan.