✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ya auri mata 9 a lokaci guda don nuna musu soyayya

Angon mai suna Arthur O Urso, an ce kyakkyawa ne da ya zama abin koyi.

Sunan wani dan kasar Brazil ya shiga cikin littafin Kundin Tarihi na Duniya bayan da ya auri mata tara a lokaci guda.

Angon mai suna Arthur O Urso, an ce kyakkyawa ne da ya zama abin koyi kamar yadda manema labarai suka ruwaito.

Ya ce ya yi haka ne don nuna soyayya da nuna adawa da auren mace daya. An daura auren ne a wani cocin Katolika da ke birnin Sao Paulo a kasar Brazil.

Tun farko dai Arthur ya auri wata mata mai suna Luana Kazaki, kuma a lokacin da suka tafi yawon ci-amarci ne suka yanke shawara kan Arthur ya kara auro wadansu mata tara lokaci guda domin nuna cewa soyayya ta kowa da kowa ce.

Majiyoyi daga shafukan Intanet sun ce, Arthur da matarsa Luana an san su a fannin soyayya. Ma’auratan kuma sun shahara ta hanyar raba hotunan batsa lokacin da suke hutun cinamarcinsu a wani gari mai suna Cap D’Agde da ke Faransa wanda ya kasance bariki.

A cikin birnin na Faransa wanda ake ta magana a kansa. an haramta sanya tufafi, hakan ya sa dukkansu suka ji dadin tafiya tsirara a wurare daban-daban na yawon bude-ido a birnin.