✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Ya bindiga sun sanya wa Sakkwatawa wa’adin biyan haraji

Sun ba da wa'adin ranar Juma'a ga al'ummomin su kammala biyan harajin.

’Yan bindiga sun sanya wa wasu al’ummomi haraji a Jihar Sakkwato inda suka ba su wa’adin kammala biyan kudaden a wannan makon.

Aminiya ta gano cewa ’yan bindigar sun hana manoma zuwa gonaki a yankunan, suka kuma shaida wa mazauna cewa idan ba su biya harajin ba zuwa ranar Juma’a, to za su kai musu hare-hare.

“An ba wa duk kauyukan wa’adin ranar Juma’a su biya kudaden ko kuma a kai musu hari. Haka mutane za su biya saboda ba su da wani zabi,” a cewar majiyarmu.

– Matakan biyan haraji

Mazauna yankin sun shaida wa Aminiya cewa bata-garin sun rika yin la’akari da yawan al’ummar kowane kauye a yankin da abin ya ritsa da su wajen yanka musu harajin da za su biya.

Binciken da muka ganadar ya nuna an sanya wa kauyukan Attalawa, Danmaliki, Adamawa, Dukkuma, Sardauna da Dangari harajin N400,000 kowannensu. 

“Kauyen Kwatsal an sa musu harajin Naira miliyan hudu, kuma har sun biya Naira miliyan biyu.

“Wasu kauyukan kuma N400,000 aka ce su biya, wasu N700,000 wasu kuma kasa da hakan, mutanen yankunan ne suka san yadda za su hada kudaden.

“A wasu kauyukan kuma, maza magidanta an sa musu N2,000 kowannensu, marasa aure kuma N1,000,” a cewar wata majiya.

– Biyan haraji shi ne mafita

Aminiya ta gano cewa mutanen yankunan na fadi-tashin nema wa kansu mafita ta hanyar biyan kudaden ne bayan sun cimma yarjejeniya da ’yan bindigar da suka yanka musu harajin.

Dan majalisar dokoki mai wakilatar Sabon Birni ta Arewa a Majalisar Dokokin Jihar Sakkwato, Aminu Almustapha Gobir, ya tabbatar da hakan, yana mai bayyana cewa an daina kai hare-hare a yankin Sabon Birni a baya-bayan nan ne saboda mutane na bin umarnin ’yan bindigar.

Ya ce, “Mutane sun gwammace su biya kudaden su zauna lafiya a kauyukansu maimakon su dogara da jami’an tsaro ko su yi kaura daga garuruwansu zuwa wasu wurare.”

– ‘Wannan ba mafita ba ce’

Tsohon Shugaban Karamar Hukumar Sabon Birni, Idris Muhammad, ya soki biyan kudaden harajin da cewa babu tabbacin kariyar rayuwar mutanen kauyukan.

“Gungu-gungu daban-daban ne ke wannan ta’asar, idan ka biya wancan gungun wane tabbaci kake da shi cewa wani gungun ba zai kawo muku hari ba?” 

“Abin da ya faru ke nan an kauyukan Gatawa da Tarah, bayan sun biya haraji, wasu gungu kuma suka kai musu hari suka yi garkuwa da mutane da dama. Sai da dangin mutanen da aka sace suka biya kudaden fansa aka sako su. 

“Abin da zai rika faruwa ke nan idan suna sa haraji mutane na biya, wasu daban za su zo su kawo hari ko su ce su ma sun sa haraji, sai an biya,” inji shi. 

Wakilinmu, ya tuntubi Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Sakkwato, ASP Sanusi Abubakar, da Kwamishinan Tsaron Jihar, Kanar Garba Moyi (ritaya), amma cikinsu babu wanda ya amsa kiran wayar wakilin namu ko rubutaccen sakon da ya tura musu.