✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ya biya ’yan bindiga su yi garkuwa da mahaifinsa

Ya yi musu alkawarin karin kudi idan aka biya kudin fansar mahaifinsa.

Dubun wani matashi mai shekara 25 ta cika bayan ya dauki hayar ’yan bindiga sun yi garkuwa da mahaifinsa mai shekara 60 domin karbar kudin fansa.

An gano cewa matashin wanda dan asalin kauyen Rinjin Gora ne a Karamar Hukumar Matazu ta jihar ya biya ’yan bindigar ne N20,000 cewa su sace mahaifin nasa, bisa alkawarin zai kara musu N200,000 bayan an biya kudin fansa.

Kakakin Rundunar ’Yan Sanda Jihar Katsina, SP Gambo Isa, ya ce duk da cewa an kama saurayin, har zuwa ranar Juma’a an kasa gaon inda mahaifin yake, amma ana ci gaba da bincike.

SP Gambo Isa ya kuma gabatar da wasu mutum hudu da aka kama ’yan bindiga suna aiken su sayo musu kayayyaki.

Ya ce an kama mutanen ne a wani samame da jami’an tsaro suka kai a wani wuri da aka zargin barauniyar hanya ce da ’yan bindiga suke bi a yankunan Safana, Kankara, Danja da kuma Makera-Funtua .

“An kama mutum hudu da ake zargi suna kai wa ’yan bindiga man fetur, sayar musu da shanun sata da kuma zuwa banki su sa musu kudi ko su ciro musu” inji shi.

An kuma kama wani “Mai shekara 50 daga kauyen Dan Jibga a Karamar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara a kan hanyar Sheme zuwa Yankara dauke da tankuna uku na injinan janareto makare da man fetur da ake zargin zai kai wa ’yan bindiga ne.” 

Jami’in ya ce da zarar an kammala bincinke za a gurfanar da mutanen da ake zargin a gaban kuliya manta sabo.