✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya dace a ci gaba da ba tsofaffin gwamnoni fansho?

A kwanakin baya ne tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Abdulaziz Yari ya nemi Gwamnantin Jihar ta biya shi kudin alawus dinsa na Naira miliyan 10…

A kwanakin baya ne tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Abdulaziz Yari ya nemi Gwamnantin Jihar ta biya shi kudin alawus dinsa na Naira miliyan 10 duk wata a matsayinsa na tsohon Gwamna. Hakan ya sa Gwamnan Jihar Bello Matawalle ya sanya hannu a sabuwar dokar da Majalisar Dokokin Jihar ta gabatar na dakatar da biyan wannan makudan kudi a matsayin fansho ga tsofaffin gwamnoni da mataimakansa. Lamarin ya tayar da kura, inda aka zakulo yadda tsofaffin gwamnoni a jihohin Najeriya suke wawushe lalitar jihohinsu. Wanan ne ya sa wakilan Aminiya suka zagaya don ra’ayoyin mutane kan ko ya dace a rika biyan tsofaffin gwamnonin wadannan kudade, kuma ga abin da suke fada:

Bai dace a ci gaba da biyansu fansho ba – Sa’eed Ahmad Sa’eed

Daga Ahmad Ali, Kafanchan

“Gaskiya a halin da Najeriya take ciki bai dace a ci gaba da biyan tsofaffin gwamnoni kudin fansho ba. Akwai kananan ma’aikatan gwamnati wadanda suka yi ritaya da ya kamata a ce ana biyansu kudin fansho amma ba a biyansu hakkinsu kamar yadda ya dace. Misali tsofaffin sojoji da suka sadaukar da rayuwarsu wajen kare kasa da tsofaffin malamai da sauransu. Muna fuskantar kalubale da dama inda ta kai wadansu gwamnoni ma ba su iya biyan albashi, ga matasa da suka gama makaranta an kasa samar musu aiki, ga mummunan talauci da ya addabi al’umma, makarantu da asibitoci an kasa gyara su, muna da karancin hanyoyi masu kyau a kasar nan, ga maganar rashin tsaro, ana ta garkuwa da al’umma gwamnati ta kasa yin komai. To a nawa tunanin ya kamata a daina biyan tsofaffin gwamnonin kasar nan kudin fansho, wannan irin kudade da ake ba su za a iya amfani da su wajen inganta rayuwar al’ummar kasar nan.”

Ko sisi bai kama a rika biyansu ba – Alhaji Sule Gaya

Daga Musa Kutama, Kalaba

“Ni  idan ta ni ne ko sisin kwabo kada a kara ba su. Mutanen da sun shafe shekara takwas suna mulki, sun kwashi kudin talakawa son ransu yadda su da ’ya’yansu babu wanda zai yi talauci, sannan a ce a ci gaba da ba su kudin fansho? Gaskiya ci gaba da ba su zalunci ne. Ba na goyon baya a ci gaba da ba tsofaffin gwamnoni kudin fAnsho.”

Wallahi bai dace ba – Danbaba Aliyu

Daga Musa Kutama, Kalaba

“Wallahi bai dace ba a ci gaba da ba su domin zaluntar talaka ake yi. Dalili shi ne ka shekara takwas kana mulki ka kwashi kudaden jama’a ka boye daga kai sai ’ya’yanka sannan a ce kuma yanzu a ci gaba da ba ka kudin fansho. Ni ban yarda da wannan  ba domin zalunci ne.”

Su amayo na baya – Murtala Abban Zahra

Daga Ahmed Ali, Kafanchan

“Wannan tambaya ce mai kyau. Wato ba maganar ya dace a rika biyan Naira miliyan 10 ga duk wanda ya yi Gwamna na shekara hudu ko takwas kawai ba ce, a’a ana maganar kwata-kwata ma ya dace ne ko bai dace ba? Idan muka duba kusan kashi biyu bisa uku na tsofaffin gwamnonin kasar nan ko dai suna Majalisar Dattawa ko sun taba yin ta. Shin a haka suke kwashe wancan kudi sannan su dawo a ba su wannan a jihohinsu saboda rashin tausayi? A ra’ayina gaskiya duk wanda ya karbi kudin nan to a tilasta masa ya biya ko in har za a ci gaba da biya to a rage kuma daga yanzu a yi doka a kan in har kana son a rika biyanka kudin fansho to babu damar sake yin takara kowace iri bayan ka bar Gwamna. Matsalar kasar nan fa kaf tana wajen tsofaffin gwamnonin nan ne.”

A nawa ra’ayin bai dace ba – Ibrahim B

Daga Amina Abdullahi, Yola

“A gaskiya bai dace tsofaffin gwamnoni su ci gaba da karbar fansho ba. Ai sun tara dukiya da yawa, don haka me za su yi da kudin fansho? Ya kamata kudin fanshonsu a rika amfani da shi wajen tallafa wa talakawa. Ko wajen gina asibitoci da  gyara hanyoyi. Ba su fansho ai kamar kara wa mai karfi, karfi ne. Don haka a ra’ayina bai dace a rika biyan tsofaffin gwamnoni kudin fansho ba.”

A ra’ayina ya dace–Ahmed Innocent

Daga Amina Abdullahi, Yola

“A ra’ayina na dan kasa ina ganin ya dace a ci gaba da biyan tsofaffin gwamnoni fansho. Dalilina shi ne ai sun yi wa jihohinsu bauta bayan haka, suna da ’yancinsu na ’yan kasa don haka dole ne a cicgaba da biyansu kudin fansho. Wannan shi ne ra’ayina.”