✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya dace gwammati ta kara harajin kayayyakin amfanin yau da kullum (BAT)?

Gwamnati Tarayya tana shirin kara harajin kayayyakin amfanin yau da kullum (BAT) daga kashi 5 zuwa kashi 7.5 domin ta kara samun kudaden shiga, musamman…

Gwamnati Tarayya tana shirin kara harajin kayayyakin amfanin yau da kullum (BAT) daga kashi 5 zuwa kashi 7.5 domin ta kara samun kudaden shiga, musamman wajen gwamnatocin jihohi sun samu damar biyan mafi karacin albashi da Gwamnatin Tarayya ta kudiri niyyar yi. Wakilanmu sun jiwo ta bakin mutane a kan wannan yunkuri:

 

Bai kamata a kara harajin kayayyaki ba – Ahmed Isa Tahir

Daga Ahmed Mohammed, Bauchi

A gaskiya bai kamata Gwamnatin Tarayya ta kara kudin harajin kayayyaki (BAT) ba, saboda gaskiya in ta yi wannan karin talaka zai ci gaba da shiga cikin azaba ne saboda hauhawar farashin kayayyaki. An yi karin kudin fetur mutane sun wahala kuma suna kan wahala ba sauki lamarin. Bai kamata a kara ba gwamnati ta nemo abin da zai sauwaka wa ’yan Nijeriya rayuwa ba tsawwala musu ba.

 

Ban zan so a kara harajin ba – Muddassiru Abdullahi Kasuwar Garki

Daga Muhammad Aminu Ahmad

Ra’ayina gaskiya ba zan so a kara wannan haraji ba, domin jama’a za su shiga cikin wani matsin rayuwa. Domin kusan komai na amfanin yau da kullum zai kara kudi, kuma mu ’yan kasuwa za a fara zargi. Don haka kamata ya yi gwamnati ta lalubo wasu hanyoyi da za ta bunkasa kudaden shigarta ba, sai an kara sa talaka cikin mawuyacin halin rayuwa ba.

 

Karin zai zama cin amanar talakawa – Isa Jalo

Daga Magaji Isa Hunkuyi, Jalingo

Gwamnati ta bar wannan batu, domin zai haifar da karin matsala ga ’yan Najeriya musamman talakawa.

Akwai kudin da Gwamnatin Tarayya ta ce ta karbo daga hannun wadanda suka wawure kudaden gwamnati da kuma kudaden da aka dakile sace su ta hanyar hade ma’ajiyar kudaden Gwamnatin Tarayya a wuri daya, wato (Single Treasury)

Maimakon kara kudin harajin kayyayaki a yi amfani da wadannan kudade wajen gudanar da ayyukan gwamnati.

Zai zama cin amanar talakawa wadanda suka zabi Buhari da nufin samun saukin rayuwa, in har Shugaba Buhari ya amince da karin kudin harajin kayyayaki

 

Karin zai kara sa talaka cikin kunci – Sanusi Sarki

Daga Ahmed Mohammed, Bauchi

A gaskiya wannan abu da gwamnati take so ta yi na kara harajin kayayyaki zai kara tsawwala rayuwa ne kawai ga talaka. Karin ba ya da wani amfani idan gwamnati ta kara talaka ne  zai dandana kudarsa, saboda komai a kasuwa zai kara kudi. An kara kudin man fetur an rufe iyaka. Ya kamata Shugaban Kasa da masu ba shi shawara su ji tsoron Allah! Ba mu zabe shi don mu rika shan wahala ba, ya kamata ya yi kishin talaka ya taimaki ’yan Arewa da ’yan Najeriya su samu sauki ba kullum a rika gana musu azaba da karin haraji ba.

 

A yi karin in zai taimaka wajen bunkasar tattalin arziki – Iliyasu Baba Kasuwar Garki

Daga Muhammad Aminu Ahmad

Ni ra’ayina gaskiya yana da kyau a yi karin harajin, muddin zai kawo ci gaban da ake bukata, kuma mu ’yan kasuwa gwamnati ta taimaka mana da jari, musamman mu kananan ’yan kasuwa, wanda yin hakan kan iya bunkasa tattalin arzikin Najeriya.

Ka ga mu ’yan kasuwa a yanzu ko da kudinka ma, kana son ka sayi kayan amma wani lokaci sam babu. In dai wannan karin harajin zai sa kayayyaki su samu, ina goyon bayan a yi shi, don zai kawo mafita gare mu.

 

Talakawa za su cutu – Ahmed Umar Gassol

Daga Magaji Isa Hunkuyi, Jalingo

Karin Haraji Kayyayakin Bukatu (BAT) zai haifar da tsadar kayyayaki kuma hakan zai kara radadi ga talakawan kasar nan A yanzu da yawa daga cikin al’ummar kasar nan ba sa iya samun abubuwan lalurar rayuwa.

Saboda haka Gwamnatin Tarayya ta tsayar da wannan shirin domin talakawa ne za su cutu.