✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya datse hannun wani saboda ya zagar masa budurwa

’Yan sanda a jihar Nasarawa sun kama wani matashi mai shekaru 21 bisa, zarginsa da laifin datse hannun wani saboda zagin budurwarsa. Kakakin rundunar a…

’Yan sanda a jihar Nasarawa sun kama wani matashi mai shekaru 21 bisa, zarginsa da laifin datse hannun wani saboda zagin budurwarsa.

Kakakin rundunar a jihar, DSP Ramhan Nansel ya ce lamarin ya faru ne ranar Juma’a a karamar hukumar Karu, inda ya yi amfani da adda ya datse hannun matashin.

Kazalika ya ce an kamo shi ne ranar Asabar, kuma ya amsa laifinsa.

Sai dai wanda ake zargin ya ce ya yi hakan ne bayan matashin ya zagi masoyiyarsa.

Danladi ya kuma ce Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar, Adesina Soyemi ya ba da umarnin mai da lamarin zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na rundunar, domin ci gaba da bincike.

Ya kuma ce da zarar an kammala za a maka shi a gaban kotu.