✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya guje wa matarsa bayan ta haifi tagwaye sau 5 a jere

Ayayin da wasu kan iya ba da kudi masu yawa domin ganin sun samu haihuwar koda da daya ne, wasu kuwa ba su ma son…

Ayayin da wasu kan iya ba da kudi masu yawa domin ganin sun samu haihuwar koda da daya ne, wasu kuwa ba su ma son ganin matansu suna haihuwa.

A kasar Uganda, an samu wani magidanci da ya tattara kayansa ya gudu daga iyalinsa, bayan da matarsa ta haifi tagwaye sau biyar a jere.

Matar mutumin mai suna Nalongo Gloria, a kwanan nan ta haifi ’ya’yanta na tara da na 10 zuwa wannan duniyar, wanda aka ce hakan ya sa mijinta, mai suna Ssalongo ya tattara kayansa ya gudu, yana mai cewa, “haihuwar ba ta lafiya ba ce kuma ba zan iya kula da ita da ’ya’yanmu ba nan gaba.”

Matar ta ce, “lokacin da na sake samun juna biyu na tagwaye, mjina ya ce wannan ya yi masa yawa kuma ya ce in koma gidanmu, inda ya yi min kora da hali kuma ba ni da lambobin wayarsa saboda na zo Kampala yin aikatau a matsayin yarinyar gida. Ya gaya min cewa idan ba zan iya haihuwar daya ba, ba zai iya kula da ni ba.”

Ta ce wata rana ta dawo gida sai ta gane cewa mijinta ya tattara kayansa ya tafi. Tun daga lokacin ba ta ji duriyarsa ba kuma tana ta fafutukar kula da ’ya’yansu.

Duk da haka ba ta yi nadama ba ga yin haihuwar kuma ta mika bukatunta ga Allah.

“Ba na nadamar haihuwar duk wadannan yaran. Na san mahaifinsu ba ya son su amma ba zan iya watsi da su ba. Duk da kalubalen da nake fuskanta, ba zan taba barin yarana ba. Ina da yakinin Allah zai yi mana tanadi.

“Na sha wahala amma Allah ne Ya san mafita,” inji Gloria A halin yanzu Nalongo tana zaune tare da ’ya’yanta bakwai, bayan manyan tagwayen biyu sun bar gidan kuma daya daga cikin sauran ’ya’yanta ya mutu a wani hadari.

Suna fuskantar makoma mara tabbas, domin mai gidan da suke haya a kwanan nan ya bayyana wa matar cewa ba ya son ganinta a gidan ko kayanta.