✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ya gurfanar da matarsa a gaban kotu bisa zargin yunkurin kashe shi

Magidancin ya roki kotu ta raba auren, tun kafin matar ta shi ta zama ajalinsa.

Wani magidanci mai suna Yemi Ogayemi, a yankin Jikwoyi dake Abuja, ya gurfanar da matarsa a gaban kotu bisa zargin barazanar kashe shi da ya ce tana yi.

Magidancin ya bukaci kotu ta raba aurensa da matar saboda gudun mummunar kaddara.

Yemi ya shaidawa kotun cewa, “Ba zan iya ci gaba da zama da matar dake son ganin bayana ba.

“Mun sami sabani kadan, kawai sai ta dauki wuka zata yanke ni, ba wani bata lokaci na tsere.

“Daga nan ta ce idan ban dawo ba, zata yanki kanta sai ta ce ni ne na yanke ta da wukar.

“Ina rokon wannan kotun da ta raba wannan auren kafin wata rana ta kashe ni ko ta kashe kanta,” cewarsa.

Bugu da kari, magidancin, ya kuma bayyana wa kotun yadda matar ta yanka masa kaya da almakashi saboda ta bukaci N7,000 a matsayin kudin gyaran gashi.

“Ta bukaci na ba ta N7,000 za ta gyara gashinta, na bata N3,000 saboda shi ne abin da nake da shi.

“Ta amsa bata ce komai ba, bayan na dawo na tarar duk ta lalata min kaya da almakashi,” inji shi.

Da take mayar da jawabi a gaban kotun, Misis Fummi, ta amsa laifukan nata, tare da neman afuwar mijin nata.

“Na roke shi kan ya yafe min, kuma ya ce ya yafe min, amma ban san me yasa ya sake tada maganar ba,” in ji Fummi.

Alkalin kotun, Jamilu Jega, ya dage ci gaba da sauraron shari’ar har zuwa ranar 9 ga watan Maris na 2021.