Daily Trust Aminiya - Ya hada baki an yi garkuwa da dan uwansa
Subscribe

‘Yan bindiga

Ya hada baki an yi garkuwa da dan uwansa

Wani mutum da ya hada baki aka yi garkuwa da dan uwansa domin karbar kudin fansa a Jihar Taraba ya shiga hannu.

Kakarin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Taraba, David Misal ya shaida wa Aminiya cewa mutumin mai shekara 43 ya bayar da bayanai kan zirga-zirgar babban wansa domin a yi garkuwa da shi a watan Agusta.

Ya ce mutumin na cikin wadanda aka tattauna da su domin biyan Naira miliyan bakwai domin fansar dan uwan nasa.

Bayan ’yan sanda masu bincike sun titsiye shi, wanda ake zargin ya shaida musu cewa N200,000 kawai masu garkuwa da dan uwan nasa suka ba shi a matsayin kasonsa bayan sun sako wan nasa.

More Stories