✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya halasta mai azumi ya sha abun kara kuzari —Sheik Lawan Abubakar

Matasan Kano sun dukufa shan kayan kara kuzari don kar azumi ya wahalar da su

Fitaccen malamin Islama a Jihar Kano, Malam Lawan Abubakar, ya ce ya halasta ga mai azumin ya sha kayan kara kuzari.

Babban Limamin na Masallacin Triump a Kano, ya bayyana hakan ne a yayin da tsananin zafin rana ya wa matasa a Jihar suke shan abubuwan kara kuzari a lokacin Sahur, saboda kar azumi ya walahar da su a watan Ramadan din bana.

Malam Lawal ya ce, “Jiki na bukatar kuzari domin gudanar da harkoki. Matukar babu giya a ciki, kuma ba ya bugarwa, azumin mutum na nan,” idan ya sha ne a lokacin Sahur ko bayan dude-baki.

Yadda matasan Kano ke rububin kayan

Matasa a Kano na amfani da kayan kara kuzari iri-iri, ganin yadda a watan azumin Ramadan din bana inda zafin ranar ke kaiwa maki 38 a ma’aunin Celcius a garin a wasu ranaku.

Matasan da Aminiya ta zanta da su sun shaida mata cewa kayan kara kuzarin na taimaka musu su kai azuminsu ba tare da sun galabaita ba.

Sani Musa ya ce, “Nakan sha Kukubima ne kawai a lokacin Sahur saboda da rana in kasance cikin kuzari ba tare da na jigata ba. Yana taimakawa sosai saboda mutum ba zai ji gajiya ba.”

Wani wanda ya kira kansa Abdul ya ce, “Zafin rana ta yi yawa kuma kullum sai na je kasuwa, sannan ina bukatar kuzarin yin aiki yadda ya kamata. Wani lokaci nakan sha bayan bude-baki, wani lokaci kuma a lokacin Sahur.”

Wani babban shagon sayar da magunguna ya shaida mana cewa cinikin kayan kara kuzarin da suka hada da sunadarai da kayan sha kwalba, ya karu a watan Ramadan din bana.

Ya kara da cewa hatta cinikin ruwan gishiri da sukari na ORS ma ya karu, saboda yana taimakawa wajen samar da ruwa a jiki musamman a watan Ramadan din da rana ke da zafi sosai.