✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ya harbe wata mata saboda doke shi a wasan kwallon kwando

Wani matashi ya harbe wata mace, Asia Womack, da ta cinye shi a wasan kwallon kwando a Amurka.

Wani matashi ya harbe wata mace Asia Womack da ta cinye shi a wasan kwallon kwando a Amurka.

Lamarin ya faru ne garin Dallas a filin wasa na wurin daukar karatu na Paul Dunar a inda ita da shi ke wasan kwallon kwando sai takaddama ta shiga tsakaninsu.

Sai Asia ta yi tafiyarta gidan kawarta, jim kadan Hogg ya bi ta gidan ya yi kiran ta, da ta fito sai ya fito da bindiga ya harbe ta.

’Yan sandan Dallas su tabbatar da faruwar lamarin a inda suka ce sun garzaya wurin da lamarin da ya faru bayan samun rahoton harbin bindiga a inda suka taras da gawar Asia a bakin titi da raunukan harsashi.

Sun kuma garzaya da ita asibitin da ke kusa, a inda ta mutu.

’Yan sandan sun bazama neman wanda ake zargi wanda ya tsere, sun kuma ci sa’ar damke shi, yana hannunsu a inda suke ci gaba da bincike.

Za kuma mika shi kotu a inda za su tuhume shi da laifin kisan kai, in ji jaridar True Crime Daily.