✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kai kyankyaso asibiti don a yi masa jinya

Likitan ya dauki nauyin kula da lafiyar kyankyason a kyauta.

Wani likitan dabbobi dan kasar Thailand ya yada wasu hotuna a shafinsa na Facebook wadanda suke nuna wani kyankyaso mara lafiya da ya ji rauni bayan an taka shi a gefen hanya, kuma wani ya tsince shi ya kai asibiti don a nema masa lafiya.

A makon jiya ne likitan dabbobin daga garin Krathum Baen a kasar Thailand mai suna Thanu Limpapattanawanich ya tsinci kansa a wani yanayi da ake neman ya ceton ran kyankyason da aka kai dakin kular gaggawa.

Wani mutum ne ya je asibiti dauke da kyankyason mai rauni bayan wani ya taka shi bisa kuskure.

Ya kai kyankyason asibitin ne don kada ya bar shi ya mutu a gefen hanya, kuma mutumin ya dauki kyankyason ne a tafin hannunsa ya kai shi asibitin dabbobi na Sai Rak.

A maimakon a yi wa mutumin da ya kai kyankyason don cetar ransa dariya, sai Dokta Limpapattanawanich ya dauki nauyin kula da lafiyar kyankyason a kyauta.

Likitan ya rubuta cewa: “A cikin dare wani ya kai kyankyason da ya ji raunin zuwa sashin kular gaggawa inda ya ce, an taka kyankyason ne a hanya.

Kuma a daidai lokacin da wannan mutumin kirki yake wucewa ne ya ga kyankyason, hakan ya sa ya hanzarta kai shi asibitin dabbobi cikin gaggawa. Yanzu kyankyason ya samu sauki da kashi 50 cikin 100 ko.”  a cewar Likitan.

“Wannan ba abun wasa ba ne domin kuwa wannan yana nuna tausayi da jinkai ga kowace halitta kuma kowane rai yana da daraja kuma ina fatar nan gaba za a samu mutane da yawa kamar haka a duniya.”

Likitan ya tabbatar da cewa wannan shi ne karo na farko da wani ya kai kyankyaso asibitin, amma babu wani abu da zai iya yi illa ya sanya kyankyason a cikin na’urar tallafa wa numfashi (oxygen) domin kara karfafa masa damar ci gaba da rayuwa.

“Na bai wa mutumin damar ya dawo da kyankyason a sake kula da shi. Ba a cajin kudin magani don jinyar kyankyason ba kwata-kwata,” inji Dokta Limpapattanawanich.

Ba a samu bayani ba kan ko kyankyason ya rayu ko akasin haka, sai dai an ce an akwai alamun nasara yayin kokarin ceto shi.

Hakan ya ratsa zukatan mutane da yawa a kafofin sada zumunta na zamani bayan yada rahoton a shafukan Facebook wanda likitan dabbobi ya yi kuma ya bazu a ko’ina.

Wannan labari ya tuno da wani labari mai kayatarwa na wata mata a kasar Isra’ila wadda ta taka wani dodonkodi bisa kuskure, kuma ta kai shi asibitin dabbobi don a gyara masa kokon bayansa