✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kamata a dauki matasa 50m aikin soji —Tinubu

"Gwamnati da ’yan bindiga da ’yan fashi na rige-rige daukar matasa aiki"

Jagoran Jam’iyyar APC na kasa, Asiwajo Bola Ahmed Tinubu, ya shawarci Gwamnatin Tarayya da dauki karin matasa miliyan 50 aikin a Rundunar Sojin Najeriya domin magance matsalr tsaro a Najeriya.

Tinubu ya yi kiran ne a jawabinsa ga taron zagayowar ranar haihuwarsa a Kano, inda ya ce yin hakan zai taimaka wa wakar wajen magance ayyukan ’yan ta’adda da masu satar mutane.

Ya ce, “Ba mu da isassu jami’an tsaro, mu da ’yan bindiga da ’yan fashi rige-rige muke yi wurin daukar matasa aiki.

“A dauki matasa miliyan 50 aikin soja, da hakan an rage abin da kasa za ta rika kashewa,” inji shi.

Ya ce, “Ba maganar jahilci ba ne, saboda duk wanda zai iya daukar bindiga ya saraffa ta, to a takaice wannan zai iya koyon gyaran taraktar noma a gona.”

Ya bayyana cewa a halin da Najeriya ke ciki matasan kasar ransu a bace yake.

Tinubu ya ci gaba da cewa, “Abin mamakin shi ne idan ka shiga kafafen sada zumunta za ka fahimci cewa matasanmu run riga sun fusata.

“Ransu ya baci, amma muna ba su hakuri da cewa za su rika sauraronsu.”

Don haka ya shawarci gwamnati da ta dauki matakan ganin tattalin arzikin kasar ya murmure ta yadda ’yan kasa za su rayu cikin sauki da walwala.