✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Ya kamata a fara yi wa duk mai mace daya bulala har sai ya kara aure’

A rika yi wa duk magidancin da ya shekara 10 da mata guda bulala 10 duk mako har sai ranar da ya kara aure.

Malam Bello Yabo ya shawarci Gwamnatin Najeriya da ta fito da wata doka da za a rika yi wa duk magidancin da ya shekara 10 da mata guda bulala 10 duk mako har sai ranar da ya kara aure.
Babban malamin addinin musuluncin da ke Jihar Sakkwato, Sheikh Bello Yabo, ya yi kira ga gwamnatin da ta fito da dokar a wani bidiyonsa da a yanzu ya karade dandalan sada zumunta musamman a Facebook.
Malamin ya bayyana cewa ya taba karantawa cewar a wata kasa ana zane duk wanda ya kai wasu shekaru da mata daya  har sai ya kara wata matar.
Hakan ce ta sanya malamin ya yi kira da Gwamnati da ta kirkiri wannan dokar a Najeriya ta zane duk wani mai mata daya har sai lokacin da ya kara aure.
Har ila yau, Malamin ya bayyana cikin raha cewa mene ne amfanin namiji ya auri mata guda, inda kuma a cikin raha ya yi kira ga ‘yan Najeriya a kan kada su sake zaben duk wani dan siyasa mai mata daya.
Sai dai wannan lamari ya jawo tafka muhawara a shafukan sada zumunta inda mutane ke tofa albarkacin bakinsu a kan jawabin malamin, inda wasu take suka yi wa malamin raddi wasu kuma suka nuna goyon bayansu a kai.
Suleiman Baba Umar  ya ce “ana maganar tsadar gero da masara da rashin kudi, amma maganar kara mata ita ce ta damu malamin”
Sai dai wasu kuma masu goyon bayan malamin sun bayyana cewa “bikin Magaji ba ya hana na magajiya” kamar yadda Abdulhamid YahuzArc ya mayar wa Suleiman martani kan sukar da ya yi wa malamin.
Wasu kuma ba su mayarwa da malamin wani martani ba, sai dai sun yi kira ga gwamnatin akan cewa bayan sanya dokar kuma ta kirkiri wata dokar ta bai wa su magidanta wani kudi na musamman domin cefanen yau da kullum.