✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kamata a yi amfani da sojojin haya a yaki ’yan ta’adda —Gwamnoni

Gawamnonin sun ce sojojin Najeriya su kadai ba za su iya yakar ’yan Boko Haram ba.

Kungiyar Gwamnonin Najeriya ta shawarci Shugaba Buhari da ya yi amfani da sojojin haya wajen yaki da ’yan ta’adda.

Gawamnonin sun ce sojojin Najeriya su kadai ba za su iya yakar ’yan Boko Haram ba.

Sun bayyana hakan ne lokacin da zuwa ziyarci Gwamnan Borno, Babagana Zulum don jajantawa bisa harin da aka kai wa manoman shinkafa a Jihar ranar Asabar.

Shugaban Kungiyar Gwamnonin kuma Gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi ya ce, “Gwamnoni ba su da kwarin gwiwa, jikinsu a mace yake.

“Hakika sojojin kasar nan kadai ba za su iya yaki da Boko Haram ba sai an samu gudunmuwa daga wasu kasashen”.

Ya ce, ba za su iya yin maganin matsalar tsaro da ta addabi wasu yankunan jihohinsu ba, da suka hada garkuwa da mutane da fashi da makami da dai sauransu.

Kayode Fayemi ya ce, “Darjar kasarmu ba za ta taba zubewa ba don mun nemi taimakon wasu kasashen kan yaki da ’yan ta’adda da ayyukan ta’addanci da ya gallabi kasarmu.

“Za mu ba Shugaban Kasa shawarar ya nemi taimakon sojojin wasu kasashen don murkushe ayyukan ta’addanci a kasar nan, saboda ta bayyana a fili cewa sojojinmu ba za su iya kawo karshen wannan matsalar su kadai ba.

“Ba kuma wai ina kalubalantarsu ba ne, ina ga hakan zai taimaka mana sosai,” inji Fayemi.

Shawarar ta zo daidai da bukatar Gwamna Zulum ga Buhari ya nemi taimakon wasu kasashen don a hada karfi wajen magance matsalar tsaro da ’yan ta’adda da suka addabi Najeriya.