✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kamata Abudllahi Abbas ya gaji Ambasada Ungogo

Tsohon Kwamishinan Ayyuka na Jihar Kano, Injiniya Muaz Magaji Dawakin Tofa ya bukaci Shugaban Buhari ya nada Shugaban Jam’iyyar APC na jihar, Alhaji Abdullahi Abbas…

Tsohon Kwamishinan Ayyuka na Jihar Kano, Injiniya Muaz Magaji Dawakin Tofa ya bukaci Shugaban Buhari ya nada Shugaban Jam’iyyar APC na jihar, Alhaji Abdullahi Abbas ya maye gurbin marigayi Ambasada Haruna Ungogo da ya rasu a kwana-kwanan nan.

Injiniya Muaz Magaji, ya ce a kokarin da ake na gyara komadar jam’iyyar APC a matakin kasa, ya dace a nada Abdullahi Abbas ya zama jakadan Najeriya.

Ya bayya cewa a maye gurbin marigayin da Abdullahi Abbas zai kawo sabbin jini a tsarin dimokuradiyya, lura da matsayin Jihar Kano na zuciyar jam’iyyar APC, kudurin uwar jami’iyyar na yin gyara da kawo sabbin tsare-tsare na shigar da hazikan matasa cikin shugabancinta.

Muazu Dawakin Tofa, ya ce Abdullahi Abbas ya yi duk abun da ya dace wurin ingantawa da gyaran jam’iyyar da kuma tabbatar da nasararta a zabukan 2015 da 2019, don haka ya cancanci mukamin.