✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kamata farashin man fetur ya haura N280 —NNPC

An saukaka farashin ne ta yadda ’yan Najeriya za su iya saya babu takura.

Kamfanin Mai na Najeriya, NNPC, ya ce ya kamata farashin man fetur ya haura Naira dari biyu da tamanin duk lita.

Yayin hirarsa da Gidan Talabijin na Channels a ranar Talata, Shugaban NNPC, Mele Kolo Kyari, ya ce akwai bukatar shi ma farashin makamashin gas wato ‘diesel’ ya haura Naira 280 duk lita, madadin farashin da ake sayar da shi a yanzu.

A cewarsa, Gwamnatin Tarayya a halin yanzu tana ci gaba da tattaunawa da Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) a kan farashin man fetur, amma babu shirin kara farashin a watan Yuli.

Wannan na zuwa daidai lokacin da farashin gangar danyen mai a duniya ya kai $74.72 a ranar Talata.

A cewarsa, ya kamata a kara farashin, sai dai Gwamnatin Tarayya ta yanke hukuncin ci gaba da sayar da shi a kan farashinsa na yanzu kafin cimma matsaya da NLC.

Kazalika, ya ce Shugaba Muhammadu Buhari, ya ba da umarnin saukaka farashin ne ta yadda ’yan Najeriya za su iya saya ba tare da sun takura ba.