✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kamata gwamnati ko masu kudi su rika tura yara karatu waje?

A baya-bayan nan  gwamnatocin jihohi da ’yan siyasa sun shiga gasar tura dalibai zuwa karatu a kasashen waje. Wannan dabi’a tana nuna yadda ’yan Najeriya…

A baya-bayan nan  gwamnatocin jihohi da ’yan siyasa sun shiga gasar tura dalibai zuwa karatu a kasashen waje. Wannan dabi’a tana nuna yadda ’yan Najeriya suke ci gaba da fifita komai na waje, inda lamarin ya shafi fannin ilimi ganin darussan da ake tura daliban su koyo duk ana koyar da su a kasar nan. Mutane da dama na ganin idan aka ci gaba da haka zai yi wuya a gyara harkar ilimin a kasar nan. Wakilanmu sun jiyo ra’ayin jama’a a kan wannan lamari kuma ga abubuwan da suke cewa:

 

Bai dace ba – Muhammad Ibrahim

Daga Musa Kutama, Kalaba

Ina! Bai dace ba to ai idan aka ce ana tura yara makaranta waje, ai makarantunmu na gida ba za su taba inganta ba. Can wane babba ne na kasar waje ka ga ya kawo dansa Najeriya karatu? Aiko daliban kasar waje ka gani a Najeriya ka bincika za ka ga ’ya’yan talakawa ne.

 

Ya kamata in dai ba siyasa a ciki – Aminu Auwal

Daga Musa Kutama, Kalaba

Ya kamata in dai babu siyasa a ciki, saboda ka ga wadansu ’yan siyasar Najeriya suna yi ne, domin su tallata manufarsu ta siyasa. Amma in dai da kyakkyawar manufa ce babu laifi, amma gaskiya kamata ya yi a daina turawa domin, idan aka ci gaba da yin haka makarantunmu na nan gida ba za a taba gyara su ba.

 

Tura su koma-baya ce –Aliyu Isah Imam Bectra

Muhammad Aminu Ahmad

Gaskiya ina kira ga gwamnati tun daga matakin tarayya zuwa Jioahi, su ji tsoron Allah a gyara makarantunmu na nan gida, a kuma ba su kula ta mussaman. Amma daukar nauyin yara zuwa karatu kasashe waje wannan koma baya ne da lalacewar al’amura, a da ai duk makarantun gwamnatin muka yi, kuma Turawa ne ke koyarwa. To mene ne dalilin da yanzu ba za mu koma kamar yadda muke a da ba. Sai dai wai gwamnati da masu kudi su rika daukar nauyin yara zuwa karatu kasashen waje, maimakon a gyara namu, su koma kamar da, a kuma kyautata wa malamai?

 

Kamata ya yi a gyara namu na gida–Aminu Salihu

Daga Lubabatu I. Garba, Kano

Ba na goyon bayan yadda gwamnati da masu kudi ke daukar yara suna kai su karatu kasashen waje. Maimakon haka kamata ya yi su yi amfani da wannan kudi wajen gyara makarantunmu a nan gida. Domin idan an duba kashi kalilan ne suke amfana da wannan tallafi yayin da dimbin dalbai suke karatunsu a gida. Amma idan aka gyara makarantun dalibai da dama za su ci moriyar abin. Ya kamata gwamnati ta tsaya tsayin daka wajen ganin ta samar da ingantaccen ilimi domin idan al’umma ta samu ilimi to rayuwar wannan al’umma za ta inganta.

 

Bai kamata a rika kashe kudi don kai dalibai waje ba –Ahmad Salihu

Daga Lubabatu I. Garba, Kano

A ra’yina bai kamata gwamnti ta rika daukar kudade masu nauyi tana biya wa yara don su yi karatu a kasar waje ba, domin hakan kashe kanmu, muke yi muna raya wadansu. Ya kamata shugabanni su duba su bi hanyoyin da za su gyara tare da farfado da harkar ilimi a kasar nan. Domin ba wai kawai makarantun gwamnati ne kadai ilimi ya tabarbare ba, hatta masu zaman kansu su ma ba wani ilimi ake samu a wurin ba.  Ya kamata a gyara mana domin mu shiga sahun kasashen da suka ci gaba a duniya.

 

A zahiri bai kamata ba–Dauda Yusuf Bulama

Muhammad Aminu Ahmad

A gaskiya bai kamata ba, saboda yau idan mai kudi ya dauki dansa ya kai waje, shi dan talaka yaya zai yi? Ba a gyara namu wadanda muke da su ba, kuma abin mamaki za ka ga cewa wannan kudi a nan Najeriya ya same su. An tura yara waje karatu ana kashe musu makudan kudade, to a maimakon haka a zo a hada hannu a gyara makarantunmu, kuma za su samu duk irin karatun da ake bukata. Idan har an inganta makarantunmu aka ba wa malamai albashi mai kyau, ko Turawan babu abin da za su nuna mana.