✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Ya kamata hutun haihuwa na mata ma’aikata ya koma wata 6’

Kungiyar ta ce hakan zai ba su damar shayar da jarirai

Wata kungiya mai zaman kanta ta bukaci Gwamnatin Najeriya da ta samar da dokar da za ta tsawaita hutun haihuwa ga mata ma’aikata mata ya koma wata shida.

Kungiyar mai suna CS-SUNN ta ce yin hakan zai ba su damar shayar da ‘ya’yansu nonon uwa zalla.

Magatakardar Kungiyar Mis Dabis Mwalike, ce ta yi wannan kiran a lokacin da take zantawa da manema labarai a Bauchi, a wani bangare na makon bikin shayarwa na duniya na shekarar 2022.

An fara gudanar da bikin ne a ranar daya ga watan Agusta zuwa bakwai ga wata, domin karfafa guiwar masu shayarwa da kuma inganta lafiyar jarirai a fadin duniya.

Ta ce, “Muna bayar da shawarwari ga ma’aikatu da kamfanoni da su ware wa masu shayarwa wani daki na musamman a wuraren aikinsu, da kuma jadawalin aikin da zai saukaka musu shayar da jariran bayan sun dawo aiki.

“Kamar yadda likitoci ke fada dai fa’idojin shayarwa sun hada da habaka tunani, da hana mutuwar mata masu juna biyu sanadiyyar ciwon daji da ciwon suga na type II,” inji ta.

Mwalike ta kuma ce, kididdiga ta nuna cewa kashi bakwai cikin 100 ne kawai na yaran da aka haifa a jihar ke samun shayarwa a sa’a ta farko, don haka akwai bukatar kara wayar da kan al’umma kan muhimmancin hakan.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, Gwamna Nasiru El-Rufa’i na jihar Kaduna shi ne Gwamna na farko a Arewacin Najeriya da ya sanar da sanya sabuwar dokar ba ma’aikata matan da suka haihu hutun wata shida tun a shekarar 2019.

Haka kuma, jihar ta kasance ta biyu bayan jihar Legas da ta tsawaita hutun haihuwar zuwa wata shidan.