✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kamata JAMB ta daina fifita ’yan Arewa – El-Rufa’i

Ya ce hakan bai tsinana wa yankin komai ba, in ban da ma mayar da dalibai malalata.

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasiru El-Rufa’i ya shawarci Hukumar Samar da Guraben Karatu a Manyan Makarantu ta Kasa (JAMB) da ta rika kayyade wa daliban Arewa maki kai daya da takwarorinsu na Kudu.

Ya bayyana hakan ne yayin tattaunawarsa da gidan talabijin na Channels ranar Litinin.

A cewar Gwamnan, hakan ne zai sa daliban su rika gogayya a kasa da ma a duniya baki daya.

El-Rufa’i ya kuma ce rufe makarantu da Jiharsa ta yi yanzu haka shi ne babban burin ’yan bindiga da sauran ’yan ta’adda, yana mai shan alwashin cewa ba za su yi nasara ba.

Gwamnan ya ce, “Arewa a ko da yaushe tana zama koma-baya a bangaren ilimi, tun bayan samun ’yancin kai, duk kuwa da fifikon da ake bamu na makin JAMB wanda bai tsinana mana komai ba. A zahirin gaskiya ma malalata ya mayar da mu.

“Ni a gani na kamata ya yi a karfafa gwiwar mutane su tashi tsaye su yi gogayya, kamar yadda muke son ganin yaranmu na Kaduna na yi, ba wai kawai a Jihar ba, har ma da a duniya baki daya.

“Mun rufe makarantu yanzu ne saboda shawarar jami’an tsaro na basu dama na wasu watanni don su shawo kan matsalar. Suna nan suna yin hakan. Muna da kwarin gwiwar cewa nan da mako biyu za mu fara shirin sake bude su.

“Ci gaba da rufe makarantu shi ne dama abin da ’yan bindiga da ’yan Boko Haram suke bukata, ba za mu bari su yi nasara ba, amma kuma ya zama dole mu kiyaye lafiyar dalibai da malamai,” inji El-Rufa’i.

Ya kuma ce nan ba da jimawa ba Jihar za ta fara shirin sake bude makarantun.