✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kamata jihohin Arewa su sake fasalin nomansu — Sa’ad Gulma

Akwai sana’o’in dogaro da kai da matasanmu za su iya yi a yanzu.

Alhaji Sa’adu Gulma dan kasuwa ne da ya mai da hankali ga harkar noma a Jihar Ogun.

A hirar da ya yi da Aminiya, ya bayyana yadda mahukunta a Jihar Legas ke kokarin yin noma domin rage dogaro da jihohin Arewa ta fuskar samar da abinci:

Mene ne takaitaccen tarihinka?

Sa’adu Gulma: Sunana Alhaji Sa’adu Yusuf Dandare Gulma kuma ni mutumin Gulma ne a Karamar Hukumar Argungu a Jihar Kebbi.

Na yi makarantar firamare ta Sabon Gari, a Gulma, na yi karamar sakandare a Kamba sannan na kammala sakandare a Makarantar Horar da Malamai da ke Argungu, sannan na yi Diploma a fannin fasahar gine-gine a Kwalejin Kimiya da Sana’a ta Jihar Kebbi a tsakanin 1989 zuwa 1990.

Daga nan sai na shiga harkar kasuwancin kayan gwari a Jamhuriyyar Benin a birnin Milabin, inda nake sayo kayan gwari daga Jihar Sakkwato in kai kasar Benin.

Na kwashe sama da shekara biyar ina harkar sai daga baya na koma Jihar Legas na samu aiki da Gwamnatin Tarayya a Ma’aikatar Ayyuka a lokacin marigayi Alhaji Lateef Jakande ne Ministan Ma’aikatar.

A wancan lokacin mu ne rukuni na farko da muka fara aiki a tsarin da ake kira ‘Direct Labour’, a karkashin wani darakta da ake kira A.Y. Shamaki, mutumin Birnin Kebbi ne.

Ina cikin aikin ne sai na ga harkar ba ta yi min ba, sai na bar aikin na koma harkar musayar kudade wato canji.

A haka ne Allah Ya hada ni da Alhaji Yahaya Abdullahi Dabi, muka fara harkar siyasa, Allah cikin ikonSa muka samu aikin samar da wajen ajiyar manyan motoci a Kasuwar Abbatuwa a nan Legas wato Tirela Fak.

Mun samu wannan aiki ne a lokacin Gwamnan Legas Raji Fashola a shekarar 2015, sannan yanzu akwai aikin noma na gwamnatin Legas wanda mun shiga ciki domin a fata a yi da mu.

An ce wajen da kuka mayar tashar manyan motoci a Abbatuwa juji ne da ake zubar da shara.

Ta yaya aka yi aikin ya cimma nasara?

Lokacin da aka ba mu aikin yin tashar manyan motoci a Kasuwar Shanu ta Abbatuwa, wannan waje da wuri ne na zubar da shara, inda ake da tarin shara da ta zama kamar dala.

A wancan lokaci babu yadda za a yi manyan motoci uku da ke kawo shanu su iya shiga su sauke shanu a lokaci guda, sai dai in wata ta shiga ta fito sannan wata ta shiga.

Amma cikin ikon Allah da muka yi aikin, a yanzu tashar na daukar manyan motoci 250, ko a watannin baya lokacin da Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Osibanjo ya zo kaddamar da aikin jirgin kasa a tashar ya sauka da jirginsa mai saukar ungulu.

Haka a wancan lokacin Gwamnan Jihar Ogun Dapo Abiodun nan ya sauka a jirgi mai saukar ungulu ya iske Mataimakin Shugaban Kasa.

Ka ga yadda muka mai da wajen zubar da shara zuwa wajen da Maitamakin Shugaban Kasa da Gwamna suka sauka da jiragensu.

Sannan yanzu mutanen da suke cin abinci kullum a cikinsa sun fi dubu 10 domin bayan tashar manyan motoci mun yi rumfuna ga ’yan kasuwa da gidajen wanka da wajen mata masu sayar da abinci da wajen sayar da man gas na manyan motoci da wajen wanke motoci da kuma karamar tasha ta kananan motoci da sauransu.

Gwmanatin Legas ta ba mu aikin ne a tsarin idan mun kammala mun mayar da kudinmu sai mu mika mata.

Gwamnatin ta bukaci mu kammala aikin cikin shekara hudu, amma Allah cikin ikonSa mun samu kammala aikin a tsawon shekara biyu da rabi, kuma wannan aiki ya kawo karshen matsalar tsaro da a baya ake fama da ita a Kasuwar Shanu ta Abbatuwa.

Ka yi maganar harkar noma a Jihar Legas da ka shiga, yaya abin yake?

Dama noma harkata ce domin ina noman shinkafa a jihohin Ogun da Kwara da Neja.

Kuma ina yi a Arewa amma a yanzu na fi ba da himmar noman a nan Kudu.

Domin a Kudun nake zaune kuma noma harka ce da ke bukatar in kana yi ka rika gani da idanunka.

Wannan aikin da nake yi ne ta fuskar noma ya ba ni damar shiga harkar noma ta Gwamnatin Jihar Legas, saboda da na ji sanarwar ban yi kasa a gwiwa ba, na yi kokari na shiga domin a yi da ni.

Sau da yawa mutanenmu na Arewa idan suka zo Kudu ba sa bai wa harkar noma muhimmanci, sai su ce sun bar noma a gida don haka ba za su yi noma a Kurmi ba.

Wannan zance na bukatar gyara domin yanayin noma a Kurmi a yanzu ba daidai yake da noman da ake yi a Arewa ba. Misali wannan yunkuri da gwamnatin Legas ta yi na bunkasa noma, ta fito da kyakkyawan tsari domin yin noman a zamanance.

Ta tanadi kayan aikin noma na zamani daga kasar China, tsarin noman da kasar China ta yi, ta wadatu da abinci, shi ne tsarin da gwamnatin Legas ta dauko.

Sun yi sanarwa duk mai bukatar shiga tsarin ko a ina yake, ko daga wane vangare yake a kasar nan ya shigo a yi da shi.

Mutum zai je Ma’aikatar Gona ta Jihar Legas ya karvi takarda ya cike, ya nuna sha’awarsa ya kuma fadi irin noman da zai yi, sai a ba shi dama, wannan tsari ya yi nisa kuma zuwa yanzu an kammala karvar takardun. Jira muke mu fara aiki gadan-gadan cikin ikon Allah.

Me ya sa Gwamnatin Legas ta fito da shirin noman?

Idan ka tuna a ’yan watannin baya Kungiyar Masu Hadahadar Kayan Abinci ta Kasa ta jagoranci yajin aiki kaurace wa kai kayan abinci Kudu, wannan mataki ya girgiza mahukunta a Kudancin kasar nan kwarai da gaske.

Don haka suka zauna suka yi nazarin yadda za su rage dogaro da Arewa ta fuskar kayan abinci ko da, da kaso 50 ne cikin 100.

Shi ya sa suka fito da wannan tsari na noma, kuma wannan aiki na Gwamnatin Jihar Legas ne, amma kowa an ba shi dama ya shigo a yi da shi, domin na san wadanda suka zo daga Arewa suka shiga, akwai wadansu daga Abuja, wadansu daga Kano da sauransu.

Yanzu haka gwamnatin Legas ta mallaki wuraren noma a Neja da Ilori, kuma tsarin noman ya shafi kowane fanni, wato noman kayan abinci da suka hada da hatsi da kayan gwari da na doya da kuma harkar kiwon dabobbi da na kifi da dodon kodi da duk wani fanni na aikin gona.

Duk wanda yake da sha’awa za a ba shi kayan aiki, idan yana bukatar bashin kudi da zai yi noman za a ba shi, sannan idan ya noma za a zo har gonar da ya yi aikin a saye kayan da ya noma.

Kuma kamar yadda na ce tsarin noma ne da za a yi shi a zamanance ba irin wanda muka sani a Arewa ba, wanda mutum zai duka ya yi ta fama.

Don haka a ganina gwamnatin Legas ta kawo mana tsarin da za mu fadada damarmu da basirarmu, kuma ina kira ga ’yan Arewa da kada su yi kasa a gwiwa su shigo a yi tafiya da su.

Maimakon tarin matasanmu da suke sana’ar tukin babur wadda a yanzu gwamnati ba ta so, kamata ya yi su yi amfani da wannan dama su shiga tsarin noma.

Akwai sana’o’in dogaro da kai da matasanmu za su iya yi a yanzu a Legas ba sai tukin babur wanda a yanzu mahukunta ke kokarin ganin bayansa.

Ba ka ganin yunkurin gwamnatin Legas kalubale ne ga manoman Arewa da gwamnonin Arewa ?

Eh, to, ba za a ce kalubale ne ga manoman ko ’yan kasuwar Arewa ba, domin suma an ba su dama za su iya shiga a yi da su.

Kuma duk abin da gwamnatin Legas za ta noma ba ya nufin ba za su bukaci na Arewa ba ne, a’a suna kokarin rage dogaro kacokan ne da Arewa.

Domin a lokacin wancan yajin aikin sun ji a jikinsu don haka suka farga domin magance wa kansu wasu matsalolin, kuma wannan yunkuri na gwamnatin Legas amfani ne ga kasa bakidaya.

Kamata ya yi gwamnatocin Arewa su rika hovvasa wajen hade kawunansu tare da vullo da dabarun kawo karshen matsalolin da suke addabar yankin.

Domin matsalar tsaro da ke addabar Arewa tana gurgunta ayyukan noma, kuma ya kamata a ce gwamnoninmu sun fito da tsarin magance haka.

Ba ka ganin yanayin kasar noma da yawan ruwan sama a Kurmi za su kawo cikas ga shirin na gwamnatin Legas?

A yanzu an samu sauyin yanayi na yawan ruwan sama a Kudancin kasar nan, yanzu ba a yawan ruwan sama na marka- marka kamar yadda ake yi a shekarun baya.

Wannan sauyin yanayi zai taimaka wa shirin gwamnatin Legas, domin a baya kalubalen da manoma ke fuskanta a Kudancin kasar nan shi ne yawan ruwan sama.

Sai a kwashe mako biyu ana tafka ruwa kamar da bakin kwarya a wancan lokaci, amma yanzu yanayi ya sauya ba a yawan ruwan kamar a baya.

Don haka akwai damar noma duk abin da ake nomawa a Arewa, yanzu haka na zo da irin albasa zan noma ta a Jihar Ogun da yardar Allah.