✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kamata Majalisar Tarayya ta hana bara a kan tituna —Ganduje

Ya ce matsalar tsaro da ake fuskanta na da nasaba da rashin neman ilimi.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano, ya ce lokaci ya yi da ya kamata Majalisar Tarayya ta hana barace-barace a ko’ina a fadin kasar nan.

Gwamnan wanda ake yi wa lakabi da Khadimul Islama, ya koka kan yadda iyaye ke tura ’ya’yansu yawon barace-barace a kan tituna, lamarin da ya ce hakan rashin imani ne.

Wannan kira na Ganduje na zuwa ne a yayin Taron Kasa karo na biyu da Tsangayar Ilimi ta Jami’ar Bayero Kano ta shirya, inda ya ce ya kamata Majalisar Tarayya ta kafa wata doka da za ta hana mabarata yawo a duk wani kwararo da sako a kasar.

A cewarsa,  “ya kamata dokar ta tilasta wa iyaye da wadanda nauyin kula da ’ya’ya ya rataya a wuyansu su rika sanya ’ya’yansu a makaranta.”

Ya kara da cewa, “matsalar tsaro da ayyukan ta’addanci da ake fuskanta a kasar nan na da nasaba da rashin neman ilimi musamman a yankin Arewa maso Gabas da wasu jihohi a Arewa maso Yammacin kasar.”