✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kamata matasa su rungumi noma ka’in da na’in – Shugaban NYSC

Gonar dai, wacce girmanta ya kai kusan hekta 16 NYSC ce ta samar da ita ga matasan domin su rika nomawa.

Shugaban Hukumar Kula da Matasa Masu yi wa Kasa Hidima (NYSC), Birgediya Janar Shuaibu Ibrahim ya shawarci matasa da su rungumi noma ka’in da na’in a matsayin hanyar dogara da kai.

Ya bayyana hakan ne yayin bikin kaddamar da shekarar noman daminar bana ta 2021 ga matasa masu hidimar kasa a Karamar Hukumar Doma ta jihar Nasarawa ranar Asabar.

Gonar dai, wacce girmanta ya kai kusan hekta 16 NYSC ce ta samar da ita ga matasan domin su rika nomawa.

Ibrahim ya ce tun shekarar 2012, NYSC ta kirkiro shirye-shiryen koya sana’o’i da ta yi wa lakabi da SAED da nufin koyawa matasan hanyoyin dogaro da kansu ba tare da sun jira aikin gwamnati ba.

Ya ce Noma na daya daga cikin sana’o’in da hukumar ke koyawa, kasancewa harkar na da karfin samarwa da dimbin ’yan Najeriya ayyukan yi.

“Muna so mu yi amfani da wannan gonar wajen karfafa gwiwar matasan domin su kara rungumar harkar noman ka’in da na’in,” inji shugaban.

Ibrahim ya kuma yabawa basaraken Doma, Aliyu Onawo saboda bayar da kyautar gonar ga hukumar domin su noma.

Ya ce hakan zai taka muhimmiyar rawa wajen  jawo hankalin da yawa daga cikin matasan domin su rungume harkar a matsayin sana’a.

“Muna kira ga sauran iyayen kasa da Gwamnatocin Jihohi su yi koyi da basaraken Doma ta hanyar bayar da gonaki ga matasan domin sa suma su gwada basirarsu a harkar noman,” inji shi.