✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kamata Ronaldo da Messi su hakura da kwallo haka —Platini

Messi da Ronaldo sun yi kuskuren sauya kungiya a bara.

Tsohon Shugaban Hukumar Kwallon Kafar Turai, Michel Platini ya sanar cewa ya kamata taurarun tamola, Cristiano Ronaldo da Lionel Messi, su hakura su ajiye kwallo haka.

Platini ya bayyana hakan ne a wata hira da jaridar La Gazetta Dello Sport, inda ya yi nazari kan makomar taurarun tamolar da suka hada Cristiano Ronaldo na Manchester United da kuma Lionel Messi na PSG.

Michel Platini yana mai kallon wadanan ’yan wasa – Cristiano Ronaldo mai shekaru 37 da Lionel Messi mai shekaru 34 a matsayin ’yan wasan da suka kafa tarihi a duniyar tamola, sai dai a cewarsa sannu a hankali sun kama hanyar bankwana da kwallon kafa a hukumance.

Dalili a cewar sa, Cristiano da Messi duniya ta shaida cewa  taurarun ne kuma kowanne daga bangarensa ya taka muhimiyar rawa a kungiyoyin da suka fi share dogon lokaci.

Gidan Rediyon Faransa na RFI ya ruwaito Platini yana cewa, daya daga cikin kuskuren da ’yan wasan suka yi a kakar shekara ta 2021 shi ne da suka canza kungiya, Cristiano ya koma da kungiyar Manchester United, yayin da Lionel Messi ya komakungiyar PSG.

Wanna zabi a cewar Michel Platini ya sa shi dogon nazari, inda tsohon tauraron kungiyar kwallon kafar Faransa ya ce shi kam, ya dau niyar ritaya daga duniyar tamola yana mai shekaru 32.

A cewarsa, a wancan lokaci yana da zabin ci gaba da taka leda da kungiyoyi irin su Barcalona ko kungiyar Marseille, sai dai a maimakon ya yi haka sai ya hakura da tamolan gaba daya.

A karshe Michel Platini ya bayyana cewa idan aka yi maganar Ronaldo sanin kowa ne Real Madrid ce ta haska shi, yayin da Lionel Messi ya haska a Barcalona.