✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kashe abokinsa da maganin bera saboda ya saci motarsa a Katsina

Ya jefa gawar abokin nasa cikin rijiya bayan ya kashe shi.

Wani malamin makaranta mai kimanin shekara 39 a duniya ya shiga hannu bisa zarginsa kashe abokinsa da guba don ya sace motarsa.

Lokacin da Rundunar ‘Yan Sandan jihar ta kama shi a Katsina, wanda ake zargin ya amsa laifin da ake tuhumarsa da aikatawa.

Da yake gabatar da wanda ake zargin a gaban manema labarai, kakakin rundunar a jihar, SP Gambo Isah, ya ce an kama shi ne a ranar daya ga watan Disamba, 2022 da misalin karfe 1:00 na rana.

Gambo ya ce, “Rundunar ta yi nasarar kama wani malamin makaranta, mai shekara 39 a Bakin Kasuwa a Karamar Hukumar Mani a Jihar Katsina, wanda ake zargi da kashe abokinsa, jami’in hukumar tsaro ta NSCDC da ke Jihar Katsina kuma abokin karatunsa na ajin karshe a Kwalejin Ilimi ta Tarayya, (FCE), a Katsina.

“Wanda ake zargin ne a ranar 26 ga watan Nuwamba, 2022 da misalin karfe 2:00 na rana, ya yaudari marigayin zuwa wani kango a Karamar Hukumar Mani, inda ya sa shi ya ajiye motarsa ​​kirar Golf mai launin shudi mai lamba AA 266 KUF.

“Ya hada masa Fura da Nono, wanda ya zuba guba a ciki.

“Bayan haka, sai ya samu wani babban itace ya daki kan wanda abin ya shafa a kai har sai da ya mutu ya jefar da gawar a cikin wata rijiya da ke cikin gidan ya lullube ta da yashi, duk da niyyar yi wa mamacin fashin motarsa.

“A yayin gudanar da bincike, an gano wanda ake zargin ya yi kuskuren kira matar marigayin ta wayar tarho cewa yana bukatar takardun motar marigayin.

“Daga baya an gano shi aka kama shi kuma ya amsa laifinsa. An samu wani fakitin maganin bera, sai wani babban itace da wata mota kirar Volkswagen Golf koriya, mai lamba AA 266 KUF, mallakar mamacin a hannun wanda ake zargin.” inji SP Gambo Isah.

Ya kara da cewa an dauko gawar mamacin daga cikin rijiyar wanda tuni ta fara rubewa, inda aka ajiye ta a asibiti domin ci gaba da bincike.