✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ya kashe kaninsa da duka

’Yan Sanda a Jihar Legas na farautar wani mutum da ya kashe kaninsa da duka saboda zargin sa da satar kaya a makaranta.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Legas na farautar wani mutum da ya kashe kaninsa da duka saboda zargin sa da satar kaya a makaranta.

Kakakin rundunar, SP Benjamin Hundeyin ne ya tabbatar da hakan, inda ya ce an sanar da DPO din caji ofis din da ke kula da yankin Ijede da ke jihar.

“Ranar Litinin ne aka kama wani matashi mai shekaru 32 da ke gadin wata makaranta ya saci talabijin guda biyar da janareta da na’urar AC da injin ban-ruwa hadi da modem.

“Da dan uwansa ya samu labari sai ya daure masa hannu da kafa ya hau dukansa har ya mutu. Ganin haka ya sa ya tsere.

“Da muka samu labarin hakan muka tura jami’anmu suka dauke gawar zuwa dakin adana gawa na babban asibitin Ikorodu, in ji shi.

Ya kuma tabbatar da za su kamo matashin don girbar abin da ya shuka.