✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ya kashe mahaifinsa kan rikicin gona

Ya yi amfani da adda ya kai masa sara a ka da kuma gadon bayansa.

Wani matashi mai shekara 32 ya kashe mahaifinsa sakamakon wani rashin jituwa tsakaninsa da wansa a daren Asabar.

Lamarin ya faru ne a wani kauye mai suna Zange cikin Karamar Hukumar Dukku a Jihar Gombe.

Bayanai sun ce mutumin mai suna Haruna Buba, ya aikata danyen aikin ne bayan wata hatsaniya ta kaure tsakaninsa da wansa bayan mahaifin nasu ya yanka wa wan gonar da ta fi wacce shi aka ba shi.

Marigayin mai suna, Habu Kuppe, dattijo ne mai shekara 70, ya gamu da ajalinsa ne a lokacin da ya yi yunkurin shiga tsakanin ’ya’yan nasa inda dan nasa ya yi amfani da adda ya kai masa sara a ka da kuma gadon bayansa.

Shaidu sun ce matashin ya yi maza ya gudu daga wajen inda ya bar mahaifin cikin jini jina-jina kafin daga bisani rai ya yi halinsa.

Mutanen kauyen sun shaida wa Aminiya cewa, Haruna Buba ya nuna karfin hali ta hanyar zarcewa zuwa gidan kallo da ke kauyen gabanin ’yan sanda su kama shi.

Embed code:

Ko da Aminiya ta tuntubi mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Gombe, SP Mallum Buba, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce an kame wanda ake zargin kuma da zarar an kammala bincike za a gurfanar da shi gaban manta sabo.