✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ya kashe mahaifinsa mai shekara 90 kan katin ATM

Wani matashi ya makure mahaifinsa mai shekara 90 ya kashe shi saboda katin cirar kudi na ATM

Wani matashi ya makure mahaifinsa mai shekara 90 ya kashe shi saboda katin cirar kudi na ATM.

Matashin mai shekara 23 ya makure mahaifinsa nasa wanda tsohon soja ne, har sai da ya mutu, a Jihar Kwara.

Kafin ya yi wannan aika-aikan, sai da ya yi wa dattijon allurar Farasitamol hade da wasu sinadaran kisa.

Hakan ne ya sa dattijon ya galabaita ba ya iya yin komai, inda shi kuma yaron ya dauke shi a kan wani babur da ya aro zuwa banki, domin sabunta masa katin ATM dinsa da kuma lambar sirri.

Kakakin ’yan sandan Jihar Kwara, Ajayi Okasanmi, ya ce bayan nan ne matashin ya dauki tsohon zuwa wani kangon gini ya makure shi ya kashe shi.

“Daga nan ya haka rami ya binne dattijon sannan ya tsere zuwa Jihar Kaduna, inda ya yi amfani da katin ATM din ya cire N59,000 daga asusun bankin dattijon,” in ji shi.

Ya ce matashin ya shaida wa ’yan sanda masu bincike cewa ya yi hakan ne saboda ya samu lambar sirri katin na mahaifinsa.

Da ya samu kuma sai ya ga ba shi da bukatar mahaifin nasa, don haka ya yanke shawarar kashe shi.

Kakakin ’yan sandan ya bayyana cewa an kuma gano cewa matsahin ya sayar da babur din da ya aro, kuma an kwato shi daga inda ya sayar.