✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ya kashe matarsa ya kokkona gawar da dutsen guga

’Yan sanda sun samu gawar matar kwance a lokacin da suka isa wajen da lamarin ya auku, kuma tuni an kai ta dakin ajiyar gawa

Wani mutum ya shiga komar ’yan sanda a Jihar Ogun bayan takaddama ta kaure a tsakaninsa da matarsa, inda ya yi ta jibgarta har ta mutu, ya kuma yi yunkunrin boye dalilin rasuwarta ta hanyar kona sassan gawarta da dutsen guga ta yadda zai samu damar cewa ta rasu ne bayan wutar lantarki ta ja ta.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ogun, SP Abimbola Oyeyemi ya ce kanwar matar ce ta shigar da kara ga ofishin ’yan sanda da ke yankin Mowe a jihar.

Ya ce mutumin da ake zargi mai shekara 51 ya yi yunkunrin boye kisan matar mai suna Folasade Badejo mai shekara 40, sai dai ’yarsa mai shekara 8 da lamarin ya auku a gabanta ta bayyana yadda mahaifinta ya kashe mahaifiyarta.

Ya ce ’yan sanda sun samu gawar matar kwance a lokacin da suka isa wajen da lamarin ya auku, kuma tuni an kai ta dakin ajiyar gawa da ke Shagamu domin gudanar da bincike.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Lanre Bankole ya ba da umarnin tura wanda ake zargin zuwa Sashin Binciken Manyan Laifuffuka na rundunar domin ci gaba da bincike.