✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya lakada wa matarsa duka har ta mutu a kan cazar waya

Ta dauki cazar ne ba tare da izininsa ba, lamarin da ya fusata shi ya fara dukanta.

Wani mutum mai suna Hassan Taiwo ya lakada wa matarsa, Chibuzor Aloh, mai ’ya’ya hudu duka har sai da ta mutu saboda ta yi amfani da cajar wayarshi ba tare da izininsa ba.

Lamarin dai ya faru ne a yankin Lugbe da ke Babban Birnin Tarayya Abuja.

Labarin rasuwar matar dai ya bulla ne a yankin ranar Lahadi.

Rahotanni sun ce matar dai ta dauki cazar ba tare da izinin mijin ba, lamarin da ya fusata shi har ya fara dukanta.

Daga nan ne ta fadi a sume, kafin makwabtanta su kawo mata dauki.

Wani mazaunin yankin wanda bai amince a ambaci sunansa ba ya ce, “Ranar Larabar da ta gabata, mijin ya lakada wa matar tasa duka saboda ta daukar masa cazar waya.

“Ya yi ta dukanta har sai da ta fadi a sume, inda shi kuma ya tafi ya bar ta.

“Daga bisani makwabtanta sun kawo mata dauki bayan da ’ya’yanta suka nemi taimako sannan har ta farfado.

“Daga baya ne muka ji cewa ashe bata je asibiti don a duba ta ba bayan farfadowar, sannan kuma ta kulle kanta a daki.

“Babu wanda ya san komai a kai. Amma ranar Lahadin da ta wuce, babban danta ya kira makwabtanta wadanda suka garzaya da ita asibiti.

“Bisa ga labarin da muka samu, ana kai ta asibitin ta mutu. Mijin kuma ya gudu, sannan ita kuma gawarta na Asibitin Kasa da ke Abuja,” inji majiyar.

Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Babban Birnin Tarayya Abuja, ASP Mariam Yusuf ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta ce suna ci gaba da bincike a kai.